Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su

Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su

- Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata, mamallakiyar wani kamfani da ke sarrafa kororon robar da aka riga aka yi amfani da su

- Rundunar, ta cafke akalla kororon roba 324,000 wadanda tuni aka wanke su, ana shirin sanyasu a kwali don shigar da su kasuwa

- A cewar matar, tana sayar da su ne a otel otel da gidajen karuwai, da ke kusa da kamfain, inda kuma ake shigar da su sassa daban daban na kasar

Rundunar 'yan sandan kasar Vietnam, ta cafke akalla kororon roba 324,000, wadanda aka riga da aka yi amfani da su, yanzu kuma ake sake gyarasu domin mayar da su kasuwa.

Rundunar 'yan sandan ta cafke buhunan kororon robar a wani gida mai lamba DX12, unguwar Hoa Nhut, gundumar Tan Vinh Hiep, yankin Binh Duong, da ke Kudancin Vietman.

KARANTA WANNAN: Sojoji sun kwato sama da mutane 20 daga 'yan bindiga a Katsina

Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su
Kororon roba a cikin ledoji bayan an kammala wankesu @lindaikeji
Asali: Twitter

A cewar jami'an rundunar, aikin mutanen gidan shine wankewa, busarwa da kuma gyara girman kororon robar, ta hanyar amfani da katago mai suffar mazakuta, kafin a shigar da su kasuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sayar da su ne a otel otel da gidajen karuwai, da ke kusa da gidan, inda kuma ake shigar da su sassa daban daban na kasar.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria

Pham Thi Thanh Ngoc, mai shekaru 33, mamallakiyar gidan, ta shiga hannun rundunar a lokacin da ta kai sumame, inda ta amsa laifinsa na karbar buhunan kororon roba sau daya a wata daga wani mutumi.

Ta yi ikirarin cewa tana tsatacewa tare da gyara kororon robar kafin sake sayar da su ga jama'a, wanda kowa zai dauka sabbi ne, a cewar jaridar VN Explorer.

Wani jami'in gwamnati ya ce: "Kororon roba na da alaka mai karfi da kiwon lafiya, don haka zamu duba laifukan da ta aika don yanke mata hukunci."

Ga hotunan kamfanin:

Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su
Ginin kamfanin da ake sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su @lindaikeji
Asali: Twitter

Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su
Buhunan kororon roba da ake shirin wanke su da gyarawa @lindaikeji
Asali: Twitter

Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su
Yadda ake gayara kororon robar bayan wanke su @lindaikeji
Asali: Twitter

Asiri ya tonu: An bankado kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su
Kamfanin da ke sarrafa kororon robar da aka riga akayi amfani da su @lindaikeji
Asali: Twitter

A wani labarin, Sama da mutane 20 da aka yi garkuwa da su, da suka hada da mata 11 da kananun yaran da ba a san iyakarsu ba, suka samu ceto daga hannun 'yan bindiga, a sassa daban na jihar Katsina.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a garin Fankama da Sabon Layi, karamar hukumar Faskari, mutane 8 ne rundunar soji ta ceto su daga 'yan bindigar, bayan samun rahotanni.

Haka zalika, rundunar soji da ke atisayen 'Sahel Sanity' sun shiga rangadi a yankin Chabas, inda suka ceto direba da mata 11 da kananan yara, da aka sacesu a kan hanyar kasuwar Batsari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel