Amurka Ta Farmaki Jirgin Iran a Teku, China Ta Fitar da Gargadi ga Trump

Amurka Ta Farmaki Jirgin Iran a Teku, China Ta Fitar da Gargadi ga Trump

  • China ta nuna damuwa kan abin da ta kira “katsalandan” da Amurka ta yi wa wani jirgin ɗaukar kaya mai ɗauke da tutar Iran a cikin teku
  • Jami'in kasar China ya bukaci dukkan bangarorin su bi yarjejeniyar tsagaita wuta da suka kulla kuma aka amince za ta kai mako biyu
  • Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Donald Trump ke cewa za a zauna a Pakistan amma Iran na cewa za ta kauracewa zaman baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya ce, Halin da ake ciki a mashigar Hormuz yana da sarkakiya.

Ya kara da cewa bangarorin da abin ya shafa su guji kara dagula al’amura, tare da samar da yanayin da zai ba da damar ci gaba da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin sauki.

Kara karanta wannan

An budewa jirgin Faransa wuta da zai wuce ta Hormuz da Iran ta toshe

Xi Jinping da Donald Trump
Shugaban China, Xi Jinping a hagu, Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gargadin China kan farmakar Iran

Reuters ta rahoto cewa China ta sake jaddada damuwarta ne a ranar Litinin bayan Amurka ta sanar da kai farmaki kan wani jirgin Iran a cikin teku.

A yayin wani taron manema labarai, Guo Jiakun ya ce ya kamata a guji kara tayar da hankali, tare da samar da sharudan da suka dace domin komawar zirga-zirgar jiragen ruwa yadda ya kamata a mashigar Hormuz.

Tun da fari, Amurka ta ce ta bude wuta tare da kwace wani jirgin Iran da ya yi yunkurin karya takunkumin da aka kakaba wa tashoshin jiragen ruwan kasar.

Sojojin Iran sun ce jirgin na dawowa ne daga China, inda suka yi alkawarin mayar da martani kan abin da suka kira “fashin teku da sojojin Amurka suka yi.”

“Yanzu wata dama ta samun zaman lafiya ta bude, ya kamata a samar da yanayi mai kyau domin kawo karshen yakin cikin gaggawa,”

Kara karanta wannan

Iran ta jingine batun zaman sulhu bayan Amurka ta kai wa jirginta hari, ta shirya ramuwa

In ji Guo.

Bayanin wani masani kan lamarin

Kwace jirgin ɗaukar kayan Iran a yankin Gulf na iya kara tayar da hankali kafin muhimman tattaunawa da za a yi a Islamabad, a cewar Amin Saikal na Jami’ar Australia

“Wadannan irin matakai na iya haifar da karin dagulewar al’amura,”

Cewar Saikal yayin hira da Al Jazeera, yana gargadin cewa matakin na iya lalata damar samun sakamako mai kyau daga tattaunawar Islamabad.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata bangarorin biyu su guji daukar matakan da za su kara dagula al’amura, musamman idan suna da niyyar cimma yarjejeniya mai dorewa.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yayin wani jawabi a kasar Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Dangane da salon Donald Trump, Saikal ya ce shugaban yana kokarin amfani da hanyoyi biyu lokaci guda, yana cewa yana son warware rikicin, amma a lokaci guda yana barazana ga Iran, wanda hakan ke kara dagula lamarin.

An farmaki jirgin Faransa a teku

A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin Faransa ya fuskanci harbe-harbe da aka ce na gargadi ne yayin da ya zo zai wuce ta mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz bayan ta zargi Trump da karya sharadi

Hakan na zuwa ne bayan dakarun Iran sun sanar da cewa sun toshe mashigar a ranar Asabar saboda zargin da ta yi wa Amurka na karya yarjejeniya.

An bayyana cewa matukan jirgin na cikin koshin lafiya duk da harbe-harben da aka ce an yi, amma sai dai wasu rahotanni sun ce jirgin ya samu matsala a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng