Darajar Naira Ta Kara Sukurkucewa, Ta Yi Faduwar da ba Ta Taba Yi ba tun Janairun 2026
- Naira ta rasa N25 a kasuwar 'yan canji ranar Laraba, inda aka riƙa sayar da dala kan N1,470, mafi ƙarancin darajarta tun 28 ga Janairu.
- A kasuwar canji ta gwamnati, Naira ta faɗi zuwa N1,363.23 kan dala, yayin da ajiyar kuɗaɗen waje ta Najeriya ta ragu da dala biliyan 1.92
- Babban Bankin Najeriya (CBN) da kamfanin NNPCL sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin ƙarfafa shigar kuɗaɗen waje da daidaita tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Darajar Naira ta sake faɗuwa a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta 'yan canji ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026 inda aka riƙa musayar dala kan N1,470.
A ƙarshen hada-hadar ciniki, Naira ta yi asarar N25, kwatankwacin 1.73% cikin 100%, idan aka kwatanta da N1,445 kan dala da aka samu ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026.

Source: UGC
Darajar Naira a kasuwar 'yan canji
Masu sana’ar canjin kuɗaɗe a Legas, waɗanda aka fi sani da Bureau De Change, sun bayyana cewa suna sayen dala kan N1,450, sannan suna sayar da ita kan N1,470, cewar rahoton jaridar TheCable.
Wannan sabon farashin shi ne mafi ƙarancin darajar da Naira ta taɓa samu a kasuwar 'yan canji tun ranar 28 ga Janairun 2026.
A ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026 an riƙa musayar dala kan N1,430, idan aka kwatanta da N1,390 da aka samu ranar 13 ga Nuwamba.
Hakan na nufin Naira ta yi asarar N40, kwatankwacin 2.88% cikin 100%, a tsakanin waɗannan ranaku.
Naira ta kuma yi rauni a kasuwar gwamnati
A kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta gwamnati, Naira ma ta samu koma baya, inda darajar dala ta kai N1,363.23.
Bayanan kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Najeriya (NFEM) sun nuna cewa Naira ta yi asarar N7.43, kwatankwacin 0.55%cikin 100%.
Wannan ya biyo bayan farashin N1,355.80 kan dala da aka samu a kasuwar a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026.
Ajiyar kuɗaɗen waje ta Najeriya ta ragu
Bayanan Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa ya zuwa ranar 14 ga Nuwamba, ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙasar ta kai dala biliyan 43.64.
Wannan adadi ya yi ƙasa da dala biliyan 45.56 da aka samu ranar 2 ga Janairu, wanda ke nuna raguwar dala biliyan 1.92, kwatankwacin 4.21% cikin 100% tun farkon shekarar.
CBN da NNPC sun rattaba hannu kan yarjejeniya
A ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026, Babban Bankin Najeriya da kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC Limited) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
Yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa shigar kuɗaɗen waje cikin Najeriya, samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan makamashi da kuma inganta daidaiton tattalin arzikin ƙasar.

Source: Instagram
CBN ya amince a kafa sabon banki a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban ankin Najeriya (CBN) ya ba katafaren kamfanin harkokin kuɗi na duniya, JPMorgan, amincewar farko ta kafa bankin kasuwanci a Najeriya.
Matakin na babban bankin CBN na iya taimakawa wajen ƙarfafa kasuwannin kuɗi na ƙasar da kuma jawo ƙarin jarin ƙasashen waje.
Asali: Legit.ng

