"Tinubu Ya Fi Buhari Kokari"; Tsohon Gwamna Ya Kawo Dalili

"Tinubu Ya Fi Buhari Kokari"; Tsohon Gwamna Ya Kawo Dalili

  • Ayodele Fayose ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fi ta marigayi Muhammadu Buhari, bisa gogewarsa a matsayin gwamna a lokacin mulkin Buhari
  • Tsohon gwamnan ya ce cire tallafin man fetur da wasu manufofin tattalin arziki sun taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar
  • Fayose ya ambaci NELFUND da kuma sauƙin darajar dala daga sama da N1,670 zuwa ƙasa da N1,400 a matsayin wasu misalan sauye-sauyen da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya kwatanta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta magabacinsa, marigayi Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari wajen gudanar da mulki.

Fayose ya ce wannan matsaya tasa ta samo asali ne daga gogewarsa a lokacin da yake gwamna ƙarƙashin gwamnatin Buhari.

Kara karanta wannan

"Yadda tsohon shugaban ƙasa ya roki Tinubu ya goyi bayan ɗiyarsa ta zama gwamna"

Fayose ya yabi Shugaba Tinubu
Ayodele Fayose tare da mai girma Shugaba Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026.

Fayose ya ce babu cikakken shugaban ƙasa

Da yake magana kan nasarorin gwamnatin Tinubu da kuma dalilan da ya sa ’yan Najeriya za su goyi bayan neman wa’adin mulki na biyu a 2027, Fayose ya ce babu shugaban ƙasa da zai iya biyan buƙatun kowa.

“Babu cikakken shugaban ƙasa. Babu wani shugaban Najeriya da zai iya biyan buƙatun kowa. Hakan ba zai yiwu ba. Ba ma za ka iya biyan dukkan buƙatun iyalinka ba.
“Abin dariya nake ji idan mutane suka ce gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari muni. Ni na kasance mai sukar Buhari, kuma na san abin da nake faɗa. Na yi gwamna a zamaninsa, don haka na san abin da nake magana a kai.
“Idan wani da yake raye a yau ya ce Tinubu bai fi Buhari ba, ina ganin ko dai ƙiyayya ce ko kuma siyasar da aka koya masa. Ba za ka iya yabon maƙiyinka ba. Zan iya faɗin hakan.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Ya yi magana kan farfaɗowar tattalin arziki

A jawabin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023, jim kaɗan bayan kama aiki, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur.

Daga bisani, gwamnatinsa ta haɗa kasuwannin canjin kuɗaɗen waje wuri guda tare da barin darajar naira ta riƙa tafiya bisa yanayin kasuwa.

Waɗannan matakai sun haifar da sauye-sauye masu yawa a farashin man fetur da canjin kuɗaɗen waje, tare da tasiri kan tsadar rayuwa da gudanar da kasuwanci.

Sai dai Fayose ya amince cewa nasarorin gwamnatin ba su kai matsayin da kowa zai kira ta cikakkiya ba. Ya kuma ce farfaɗowar tattalin arziki bayan durƙushewa ba abu ne mai sauƙi ba.

“Tinubu ya daidaita tattalin arzikin ƙasar. Wataƙila bai kai matsayin da kowa zai ce ya zama cikakke ba, amma ana samun ci gaba. Idan abubuwa sun lalace, farfaɗowa ba abu ne mai sauƙi ba.
“Idan tattalin arziki ya durƙushe, dawo da shi kan hanya ba abu ne mai sauƙi ba. Ba na cewa Tinubu cikakke ne. Ban taɓa ɓoye goyon bayana gare shi ba, domin na san irin ƙoƙarin da yake yi.

Kara karanta wannan

APC ta yi gyara a kwamitin kamfen din Tinubu bayan an yi abun kunya a idon duniya

“Ya yi abubuwa masu kyau kawo yanzu. Amma dole ne a samu wanda zai kalubalance shi a zaɓe. Dole ne wani ya yi takara da shi, kuma ya faɗi munanan abubuwa a kansa domin samun nasarar zaɓe,” in ji shi.
Fayose ya yabawa Shugaba Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose Hoto: Ayodele Fayose
Source: Facebook

Fayose ya yi maganar yadda za a binne shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ba da wasiyya game da yadda za a birne shi bayan Allah ya karbi rayuwarsa.

Fayose ya bayyana cewa yana so a binne shi cikin mako hudu kacal bayan rasuwarsa, tare da yin cikakkiyar umarni kan yadda ake son a gudanar da jana’izarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng