Ana Tunanin Kirkirar Sababbin Jihohi 31 a Najeriya, Majalisa Za Ta Ji Ra'ayin Jama'a

Ana Tunanin Kirkirar Sababbin Jihohi 31 a Najeriya, Majalisa Za Ta Ji Ra'ayin Jama'a

  • Majalisar dattawa za ta gudanar da zaman jin ra'ayin jama'a kan duba ƙudurori 31 da aka gabatar na bukatar kafa sababbin jihohi
  • Za a tattauna batutuwa kamar 'yancin ƙananan hukumomi, kafa 'yan sandan jihohi, sauye-sauyen shari'a da ƙarfafa tsarin shugabanci
  • Kwamitin yana ƙoƙarin jin ra'ayoyin jama'a don inganta wakilcin mata a siyasa, da ba da damar tsayawa takara ba tare da jam'iyya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin majalisar dattawa da ke duba sauye-sauyen kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya ce zai yi la'akari da ƙudurori 31 da suka shafi ƙirƙirar sabbin jihohi.

Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin, ya ce za a duba ƙudurorin ne a yayin zaman jin ra’ayoyin jama’a da za a gudanar na tsawon kwanaki biyu, daga 4 zuwa 5 ga Yuli, 2025.

Majalisar dattawa za ta saurari ra'ayoyin jama'a kan kirkirar jihohi 31
Zauren majalisar dattawa yayin da sanatoci ke gudanar da zama. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Jin ra'ayoyin jama'a kan kirkirar jihohi 31

Mataimakin shugaban majalisar ya ce za a gudanar da zaman jin ra'ayoyin ne a lokaci guda a manyan sassan Najeriya kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sassan da za a gudanar da taron su ne: Legas (Kudu maso Yamma), Enugu (Kudu maso Gabas), Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu), Jos (Arewa ta Tsakiya), Maiduguri (Arewa maso Gabas), da Kano (Arewa maso Yamma).

A wata sanarwa da mai ba Barau Jibrin shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ranar Lahadi, ya ce kwamitin na da kudurin tattara ra’ayoyin ‘yan kasa a kan muhimman sauye-sauye da za a yi wa tsarin mulkin kasar.

Mudashir ya bayyana cewa kwamitin ya karɓi bukatun ƙirƙirar jihohi biyar daga Kudu maso Yamma, Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya; bukatu bakwai daga Arewa maso Gabas; guda shida daga Arewa maso Yamma; da guda uku daga Kudu maso Gabas.

Jin ra'ayi kan ba kafa hukumar zaben ciyamomi

Hadimin ya ƙara da cewa za a kuma duba batutuwa masu muhimmanci na ƙasa da suka haɗa da 'yancin ƙananan hukumomi, sauye-sauyen shari'a da zaɓe, kafa ‘yan sandan jihohi, da ƙarfafa tsarin shugabanci.

A cewarsa, daya daga cikin kudurorin na neman amincewa da ƙananan hukumomi a matsayin wani ɓangare na gwamnatin tarayya da ke da tabbataccen wa’adin mulki.

“Kudurin na biyu game da garambawul ga ƙananan hukumomi, yana neman kafa hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta da za ta shirya da gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi (NALGEC).
“Za a kuma duba wasu kudurori guda biyu kan tsaro da ‘yan sanda, da suka shafi kafa ‘yan sandan jihohi da majalisar tsaron jiha don tsara manufofin tsaron cikin gida.”

- Ismail Mudashir.

Bukatar kafa majalisun sarakunan gargajiya

A fannin sauye-sauyen kudi, za a duba kudurori shida, ciki har da wanda ke neman bai wa hukumar raba kuɗin tarayya (RMAFC) ƙarfi na musamman, inji rahoton Leadership.

An ce ana so RMAFC za ta rika tabbatar da bin ka’idojin tattara da raba kudin da ake samu daga asusun tarayya, da sauƙaƙe tsarin duba hanyar raba kudaden gwamnati.

A bangaren kasafin kudi, za a duba kuduri da ke son gyara kundin tsarin mulki domin fayyace lokacin da shugaban kasa ko gwamnan jiha zai mika kasafin kudi ga majalisar dokoki.

Kwamitin zai kuma duba kuduri na ƙara yawan kujerun mata a majalisar dokoki ta ƙasa da ta jiha, a wani yunkuri na inganta wakilcin mata a siyasa.

Mudashir ya ce kwamitin zai duba shawarar kafa majalisun sarakunan gargajiya a matakin tarayya, jiha da ƙananan hukumomi, domin ƙarfafa ginshikin sarautu.

Majalisa za ta saurari ra'ayin jama'a kan kafa majalisar sarakunan gargajiya
Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin sauye-sauyen kundin tsarin mulki. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Sauye-sauye da ake so a yi wa tsarin mulki

A bangaren sauye-sauyen tsarin zaɓe, za a duba kudurori da ke neman bai wa mutane damar tsayawa takara kai tsaye ba tare da shiga jam’iyya ba, da kuma damar yin zaɓe daga ƙasashen waje.

Har ila yau, akwai fiye da kudurori 20 da suka shafi garambawul ga tsarin shari’a, ciki har da waɗanda ke neman fayyace wa’adin yanke hukunci da faɗaɗa ikon kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe.

Mudashir ya ƙara da cewa wasu daga cikin kudurorin suna neman sauya tsarin raba iko ta hanyar cire wasu fannoni kamar aikin yi da sufurin jiragen ruwa daga jerin ikon gwamnatin tarayya zuwa ikon hadin gwiwa tsakanin tarayya da jihohi.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su halarci zaman jin ra’ayin, yana mai cewa shigar da jama’a cikin lamarin yana da matuƙar muhimmanci wajen sauya kundin tsarin mulki.

Zargin da ake yi wa APC kan kirkirar sababbin jihohi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, cibiyar ta yi zargin cewa APC na amfani da batun kirkiro sabbin jihohi a matsayin dabarar yaudarar ’yan Najeriya kafin zaɓen 2027.

Shugaban CHRICED, Ibrahim Zikirullahi, ya bayyana cewa APC na amfani da wannan shiri ne don neman farin jini, duk da cewa tasan ai ba zai yiwu ba.

Zikirullahi ya yi gargaɗi cewa ƙirƙirar ƙarin jihohi zai ƙara dagula halin tattalin arzikin ƙasar, inda yawancin jihohi ma ke kasa biyan albashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.