An Gabatar da Bukatar Kirkirar Sababbin Jihohi 31 a Najeriya, An Jero Su daga Yankuna 6

An Gabatar da Bukatar Kirkirar Sababbin Jihohi 31 a Najeriya, An Jero Su daga Yankuna 6

  • Kwamitin Majalisar Wakilai kan duba kundin tsarin mulki ya ce an gabatar da bukatun kirkiro sabbin jihohi 31 daga yankuna shida na Najeriya
  • Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ya karanta wasikar da ke bayyana sharuddan da dole ne a cika kafin a amince da kirkiro jihohi
  • Wasikar ta ce sashe na 8 na kundin tsarin mulki ya tanadi bukatun da dole ne a bi, ciki har da amincewar kashi uku na 'yan majalisa kafin kafa jiha

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kwamitin Majalisar Wakilai kan duba kundin tsarin mulki ya sanar cewa an gabatar da bukatun kirkiro sabbin jihohi 31 daga yankuna shida.

Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ya karanta wasikar kwamitin a zauren majalisa a yau Alhamis 6 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bukaci korar kwamishinonin zabe a jihohi 3 kan zargin rashin da'a a 2023

An gabatar da bukatar kirkirar sababbin jihohi 31
An karanto bukatar kirkirar sababbin jihohin 31 a Najeriya yayin zaman Majalisa. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Sababbin jihohin da ake son kirkira a Najeriya

Ben Kalu ya bayyana sharuddan da dole ne a bi kafin a amincewa da kirkirar sababbin jihohin, cewar jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar ta ce an gabatar da bukatu biyar daga Arewa ta Tsakiya, hudu daga Arewa Maso Gabas, biyar daga Arewa Maso Yamma, da wasu daga kudancin Najeriya.

Daga cikin jihohin da ake shawarar kafa su akwai Okun, Okura, Confluence (Kogi); Benue Ala, Apa (Benue), jihar Abuja.

Sauran sun hada da Amana (Adamawa) da Katagum a cikin jihar Bauchi.

Har ila yau, akwai jihar Sabuwar Kaduna da Gujarat daga Kaduna; Tiga da Ari daga Kano; Kainji daga Kebbi; da wasu jihohi kamar Etiti, Orashi da Adada.

Sai kuma sauran jihohin da aka ambata sun hada da Ogoja daga Cross River, Warri daga Delta, Ori da Obolo daga Rivers, da kuma wasu daga jihohin Ondo, Oyo, da Ogun, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya

Wasikar ta jaddada cewa sashe na takwas na kundin tsarin mulki ya tanadi sharuddan da dole ne a bi kafin a fara aiwatar da bukatar kirkirar jihohi.

Dokokin da ke cikin tsarin kirkirar sababbin jihohi

"Wasika zuwa Majalisar Tarayya don neman kirkirar sabuwar jiha za a amince da ita ne kawai idan akalla kashi uku na ‘yan majalisa suka goyi baya."
"Masu bukatar karin kananan hukumomi su sani cewa sashe na 8 na kundin tsarin mulkin Najeriya, bayan an yi gyara, shi ne zai jagoranci aiwatar da hakan."
"A cewar sashe na 8.3 na kundin tsarin mulki, sakamakon kuri'un Majalisun Jihohi a zaben raba gardama dole ne a mikawa Majalisar Tarayya."
"Bukatu za a sake mika su ne daidai da sharuddan da aka tanada, a aike da kwafin takardu uku zuwa ofishin kwamitin a dakin H331, Majalisa."

- Cewar sanarwar

Yayin karanta wasikar, Kalu ya ce:

"Kwamitin zai goyi bayan duk wani yunkuri da ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulki, kuma zai duba bukatu ne kawai da suka bi ka’ida."

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Majalisa ta amince Tinubu ya kori kwamishinonin zabe

Kun ji cewa Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na tsige kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa watau REC na jihohi uku.

Hudu Ari, kwamishinan zaɓen Adamawa wanda ya ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta samu nasara na cikin waɗanda aka kora.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.