Sanataocin Arewa Sun Yi Matsaya kan Matsalar Rashin Tsaro, an ba Gwamnati Shawara

Sanataocin Arewa Sun Yi Matsaya kan Matsalar Rashin Tsaro, an ba Gwamnati Shawara

  • Ƙumgiyar Snatocin Arewa ta nuna takaicinta kan hare-haren da ƴan bindiga suka kai a jihar Benue waɗanda suka jawo asarar rayuka
  • Sanatocin sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta samar da isassun kuɗi ga rundunonin sojoji domin sayo kayan aiki na zamani
  • Ƙungiyar ta kuma yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ziyarar jaje da ya kai a Benue sakamakon hare-haren ƴan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar sanatocin Arewa (NSF) ta ba gwamnatin tarayya shawara kan matsalar rashin tsaro da aka yi shekara da shekaru ana kuka da ita.

Sanatocin na Arewa sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta samar wa rundunonin sojoji da sauran hukumomin tsaro kayan aiki na zamani domin yaƙi da ta’addanci da ƴan bindiga faɗin ƙasar nan.

Sanatocin Arewa sun ba gwamnatin tarayya shawara
Sanataocin Arewa sun bukaci a ba sojoji kayan aiki na zamani Hoto: @SenateNGR
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, wacce shugaban ƙungiyar, Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, ya rattaɓa wa hannu, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin Arewa sun yi Allah da harin ƴan bindiga

Sanatocin sun yi tir da hare-haren da aka kai kwanan nan a jihar Benue, inda fiye da mutum 100 suka rasa rayukansu sakamakon harin da ake zargin makiyaya ne suka kai.

Sanatocin sun yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

"NSF na yabawa da ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai yankunan da abin ya shafa, wanda hakan ke nuna ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro."
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakai na zahiri domin tabbatar da adalci da kuma hana maimaituwar irin wannan al’amari a gaba."

- Sanata Abdul'aziz Yar'adua

Wacce shawara Sanatocin suka ba gwamnati?

Ƙungiyar NSF ta ce ya zama dole gwamnati ta ƙara kuɗi ga rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro domin su iya sayen kayan aiki na zamani da za su taimaka wajen yaƙi da ƴan ta’adda da masu tada ƙayar baya.

Haka kuma, sanatocin sun jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, inda suka buƙaci gwamnati da ta samar da hanyoyin yin tattaunawa da daidaiton aiki a tsakaninsu.

“Kungiyar NSF za ta ci gaba da haɗa kai da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalolin tsaro a ƙasar nan."

- Sanata Abdul'aziz Yar'adua

Sanatocin Arewa sun koka kan rashin tsaro
Sanataocin Arewa sun bukaci gwamnati ta kara kudade ga hukumomin tsaro Hoto: Senator Abdul'aziz Yar'adua
Asali: Twitter

A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci ƴan Najeriya da su kasance masu lura da abin da ke faruwa a yankunansu, tare da kai rahoto ga hukumomin da suka dace idan suka ga wani abu da ba su yarda da shi ba, tana mai cewa tsaro hakkin kowa ne.

Sojoji na buƙatar kayan aiki

Usman Idris ya shaidawa Legit Hausa cewa shawarar da sanatocin suka ba gwamnatin tarayya ta yi daidai.

Ya nuna cewa dole sai jami'an tsaro suna da kayan aiki sannan za su iya tunkarar barazanar rashin tsaro.

"Sanatocin sun gayawa gwamnati gaskiya domin dole sai sojoji na da kayan aiki masu inganci sannan za su iya fafatawa da ƴan ta'adda."

"Idan akwai kayan aiki na zamani za a samu damar murƙushe masu tayar da ƙayar baya cikin sauƙi."

- Usman Idris

Basarake ya magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tor Tiv na Benue, mai martaba James Ayatse, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar.

James Ayatse wanda ya yi jawabi a gaban shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ana ba da bayanai ba daidai ba kan rikicin.

Babban basaraken ya ce rikicin jihar Benue wani shiryayyen shiri ne yi wa mutane ƙisan ƙare dangi wanda aka ɗauki shekaru ana yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng