Ganduje Ya Haɗa Kai da Majalisar Tarayya, Za a Kawo Sabon Tsarin Kaɗa Kuri'a a 2027

Ganduje Ya Haɗa Kai da Majalisar Tarayya, Za a Kawo Sabon Tsarin Kaɗa Kuri'a a 2027

  • Shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin gudanarwa na jam'iyya reshen kasar Faransa a birnin Faris
  • Ganduje ya ce APC na aiki kafaɗa da kafaɗa da Majalisar Tarayya domin samar da tsarin da zai ba ƴan Najeriya mazauna waje damar kaɗa kuri'a
  • Shugabar jam'iyyar APC ta Faransa ta roki Ganduje da sauran masu ruwa da tsaki su tabbata sun cika masu burinsu na kaɗa kuri'a a zaɓe na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

France - Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki na ƙoƙarin samar da tsarin da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje za su kaɗa kuri'a a zaɓe.

Ya ce APC na aiki tare da Majalisar Dokoki ta kasa domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje sun samu damar kada kuri’a a zabubbuka na gaba.

Shugaban APC, Ganduje.
APC ta fara kokarin kawo tsarin da zai ba ƴan Najeriya nazauna kasashen waje damar kaɗa kuri'a Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Me ya kai Ganduje ƙasar Faransa?

Ganduje ya faɗi hakan ne da yake kaddamar da sabon kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC reshen kasar Faransa a birnin Paris a karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin mambobin jam’iyya a kasashen waje, yana mai cewa suna da rawar da za su taka a kokarin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai magana da yawun shugaban APC na ƙasa, Edwin Olofu, ya fitar ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Ganduje ya yabi shugabannin APC na Faransa

Shugaban APC ya ce:

“Muna yaba muku kan yadda kuke ci gaba da tallata jam'iyyarnu, kuna kara yawan mambobi da kuma taimakawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman duba da sauye-sauyen da yake yi domin farfado da tattalin arzikin kasa."

Ya ce yanzu ana samun karin kuɗaɗe don ayyukan raya kasa, kuma gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi sun shaida haka.

Ganduje ya ce APC na zaune lafiya, sabanin wasu jam’iyyu da ke fama da rikice-rikicen cikin gida, hakan ya jawo jiga-jigan siyasa da dama ke sauya sheka zuwa APC.

Mazauna kasahen waje na ba da gudummawa

A nata jawabin, sabuwar shugabar jam’iyyar APC reshen Faransa, Hajia Amina Musa Baba Suzuki, ta bayyana ƴan Najeriya mazauna kasashen waje na alfahari da ƙasarsu.

“’Yan Najeriya mazauna kasashen waje ba tara kudi da zuba jari kadai suke ba, sun kasance shugabanni kuma masu ruwa da tsaki da ke ba da gudummuwa a harkar siyasa.
"Muna ba da gudummuwa da biliyoyin Naira tare da zuba jari, sannan mu jakadu ne da ke alfahari da tsarin demokuraɗiyyar Najeriya.

- In ji Hajiya Amina

Tutar APC.
APC ta kaddamar da shugabanninta reshen kasar Faransa Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Wane aiki APC ke son Majalisa ta yi?

Ta kuma bukaci Ganduje da ya jajirce wajen ganin ƴan Najeriya da ke zaune a kasashen ketare sun samu damar kada kuri’a.

"Ba tsayawa za mu yi muna cewa ba zai yiwu ba,wannan ya zama dole, muna rokon ku cika mana burinmu kafin karewar wa'adin wannan gwamnatin," in ji ta.

Ganduje ya caccaki Buba Galadima

A wani labarin, kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya tanka Buba Galadima wanda ya ce ba shi da amfani a siyasa.

Dr. Ganduje ya bayyana cewa kalaman da Buba Galadima ya nuna ƙarara cewa shi mutum ne mayaudari wanda bai san halacci ba a siyasa.

Shugaban APC ya yabi kansa da cewa shi mutum ne da mutane suka kwada kuma su amince da rikon amanarsa da nagartarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262