Pantami Ya Samu Gagarumar Nasara a Gombe, Jigon LP Ya Mara Masa Baya
- Tsohon ɗan takarar sanata a jam'iyyar LP ya fice daga cikinta inda ya nuna goyon baya ga Farfesa Isa Ali Pantami
- Jigo a LP ya fice daga jam’iyyar tare da bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamna ƙarƙashin PDP a Gombe
- Dan siyasar ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da magoya baya, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki domin ci gaban Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Gombe - Siyasar jihar Gombe ta fara sauya salo bayan ficewar wani tsohon ɗan takarar Sanata zuwa jam'iyyar PDP.
Dr. Ibrahim Adamu Usman, wanda ya nemi takarar kujerar Sanata na Gombe ta Arewa a jam’iyyar LP, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya.

Source: Twitter
Rahoton da Leadership ya ce dan siyasar ya bayyana goyon bayansa ga takarar gwamnan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Dalilin dan siyasa na goyon bayan Pantami
Usman ya bayyana wannan matsaya ne a wani taron magoya bayansa, inda ya ce ya yanke shawarar bayan doguwar tattaunawa da magoya baya, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki daga yankin Gombe ta Arewa.
Ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne bayan Pantami ya shiga jam’iyyar PDP da kuma burinsa na bayar da gudunmawa wajen bunƙasa Gombe da Najeriya baki ɗaya.
Ya ce:
“Wannan shawara ita ce sakamakon tattaunawa mai zurfi da magoya bayana, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki daga faɗin Gombe ta Arewa."
Tsohon ɗan takarar Sanatan ya bayyana Pantami a matsayin babban malami da ƙwararren masani a harkokin tsaron yanar gizo, fasaha da kuma jagoran sauye-sauyen dijital a Najeriya.
Ya ƙara da cewa ayyukan Pantami a lokacin da yake minista, musamman wajen ƙarfafa matasa, bunƙasa al’umma da haɓaka kirkire-kirkiren fasaha.

Source: Original
Tsohon ɗan takarar ya godewa LP
Usman ya gode wa jam’iyyar Labour saboda damar da ta ba shi ta tsayawa takarar Sanata a zaɓen 2023, yana mai jaddada cewa ficewarsa ba rashin girmamawa ba ne ga shugabancin jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, Alhaji Yusuf Daudu Kaltungo, wani jigo a tafiyar siyasar Pantami, ya bayyana sauya sheƙar Usman a matsayin babban ci gaba ga yaƙin neman zaɓen gwamna na PDP.
Ya ce wannan ci gaban zai ƙara wa tafiyar ƙarfi tare da inganta damar samun nasara a zaɓen gwamnan da za a gudanar a shekarar 2027.
Haka kuma, Isa Muhammad Baba ya ce matakin da Dr. Usman ya ɗauka na nuna yadda amincewa da shugabanci da hangen nesan Pantami ke ci gaba da ƙaruwa a tsakanin al’umma.
Ita ma Aishatu Sa’idu daga ƙungiyar yaɗa labaran Pantami a kafafen sada zumunta ta ce goyon bayan tsohon ministan ya mamaye sassa daban-daban na al’umma saboda irin tarihin aikinsa a hidimar jama’a.
Pantami ya fadi dalilin fara nema takara
A wani labarin, an ji cewa tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, ya zama dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Gombe domin zaben 2027.
Pantami ya samu dubban kuri’u daga dukkan manyan mazabu uku na Gombe yayin tsarin tabbatar da dan takarar jam’iyyar PDP.
Tsohon ministan ya ce manufarsa ita ce yaki da talauci ta hanyar ilimi, noma na zamani da jawo jarin kasashen waje zuwa Gombe.
Asali: Legit.ng

