Kasar Iran Ta Canza Ra'ayi game da Tayin Trump, Ta Yi Maganar Yiwuwar Sulhu da Isra'ila
- Kasar Iran ta nuna alamun karɓar tayin shugaban Amurka, Donald Trump na zaman tattaunawa kan rikicinta da Isra'ila
- Wani jami'in Iran da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jamhuriyar Iran za ta karɓi tayin matuƙar akwai mutuntawa da kuma adalci
- A kwanakin baya dai Trump ya ce a shirye yake ya tura jami'an gwamnatinsa domin tattaunawa musamman kan shirin nukiliya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Rahotanni sun bayyana cewa ƙasar Iran na da niyyar karɓar tayin ganawa da Shugaban Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan rikicin da ke faruwa tsakaninta da Isra’ila.
Wannan bayanin ya fito ne ranar Laraba, daga wani babban jami’in diflomasiyyar Iran, wanda bai bayyana sunansa ba kawo yanzu.

Asali: Getty Images
Reuters ta tattaro cewa Iran ta nuna cewa a shirye take ta halarci tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicinta Isra'ila, wanda ke ƙara ta'azzara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iran ta sauya ra'ayi kan tayin Shugaba Trump
Ministan Harkokin Waje na Iran, Abbas Araghchi, wanda ya taka muhimmiyar rawa a tsarin diflomasiyyar ƙasar, yana daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci irin wannan ganawa idan aka cimma matsaya.
Ana sa ran taron da zai gudana zai maida hankali ne wajen tattauna batun tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra’ila.
Wannan na zuwa a wani lokaci da rikicin ya yi kamari a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da mummunan tasiri da ɓarna ga fararen hula da tattalin arziki.
Wane tayi Trump ya yi wa Iran tun farko?
Shugaba Donald Trump, wanda ya bayyana ra’ayinsa na neman tattaunawa da Iran tun farkon makon nan, ya ce burinsa shi ne a maida hankali kan shirin nukiliyar Iran.
A lokacin da yake magana da manema labarai, Trump ya ce yana shirin aikewa da wakilan Amurka domin wakiltar gwamnati a irin wannan ganawa.
"Zan iya aika Steve Witkoff ko mataimakina, JD Vance, domin su gana da jami’an Iran,” in ji Trump.
Trump da gwamnatinsa sun fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 watau JCPOA a 2018, inda suka sake kakabawa Iran takunkumai masu tsauri.
Iran na shirin shiga tattaunawa da Amurka
Idan aka cimma matsaya a wannan sabon yunƙuri, zai iya zama wani sabon babi na diflomasiyya tsakanin Iran da Amurka musamman ganin yadda rikicin Gaza da Iran-Isra’ila ke ƙara tsananta.

Asali: Getty Images
Wani jami’i daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Iran ya kara da cewa:
“Iran ba za ta kauce wa tattaunawa ba idan akwai adalci da mutunta ‘yancin kowane bangare. Muna fatan ganawa da kowa idan hakan zai kawo zaman lafiya.”
Har yanzu ba a bayyana lokaci da wurin da za a yi wannan ganawar ba, kuma Amurka ba ta fitar da wani bayani kan hakan ba, rahoton BBC.
Amurka na shirin shiga faɗan Isra'ila da Iran
A wani labarin, kun ji cewa jami'an Amurka sun fara shirye-shiryen haɗuwa da Isra'ila, su yi wa ƙasar Irana taron dangi.
Wannan na zuwa ne a yayin da rikicin tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba da ƙamari, inda kasashen biyu ke harbawa juna manyan makamai masu linzami.
Har yanzu dai Trump bai fito ya bayyana cewa zai kai wa Iran hari ba, sai dai alamu sun nuna yana goyon bayan Isra'ila a wannan gaɗa ake yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng