Yadda Jihohin Arewa ke Fafatawa wajen Yaki Da Masu Kwacen Waya

Yadda Jihohin Arewa ke Fafatawa wajen Yaki Da Masu Kwacen Waya

A yayin da matsalar masu ƙwacen waya ke ƙara ta’azzara a sassan Arewacin Najeriya, jihohin Kaduna, Gombe da Kano sun ƙaddamar da matakai na musamman don murkushe lamarin.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A baya-bayan nan, an rika samun rahotanni a kan yadda masu ƙwacen waya ke kashe mutane a jihohin, kuma lamarin ya fi kasanta a jihar Kano.

Yan sanda sun fara yakar masu fashin waya
Jihohin Arewa sun fara yaki da masu kwacen waya Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Legit Hausa ta bincika yadda hukumomin tsaro a jihohin uku ke tunkarar wannan ƙalubale domin tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.

Kano: Ana kamen masu ƙwacen waya

Rundunar ‘yan sanda ta ƙaddamar da rundunar sintiri ta musamman wato Operation Restore Peace, domin dakile yawaitar kwacen waya da daba a yankunan birni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafin Facebook cewa an cafke sama da mutane 300 da ake zargi da hannu a laifuffukan kwace-kwace da tada tarzoma.

Baya ga kwamitin, rundunar ta kuma haramta kidan gangi da wasa da makamai domin kare barkewar fadan daba, wanda ana amfani da shi wajen kwacen waya.

Yadda yan sandan Kaduna ke maganin ƙwacen waya

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar wa da Legit cewa ba za ta lamunci al'amarin ƙwacen waya ya hana jama'a zaman lafiya ba.

A zantawarmu da Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya ce daga cikin matakan da suka dauka yanzu shi ne bibiyar wadanda ake zargi da aikata laifuffuka har maboyarsu.

Ya ce:

"Mun kama, mun yi shara ta 'yan daba da sauransu, wanda muka nuna wa 'yan jarida – kusan mutum 500."
"Sai kuma abin ya fara daukar sabon salo, wanda hakan ya sa rundunarmu ta tashi tsaye. Yanzu haka, salon da muka dauka ba wai jiran su fito muke ba – muna bi su gida-gida da kuma duk wuraren da suke buya."

"Sannan, ita kanta gwamnatin jiha ta kafa kungiyar haɗin gwiwa da jami'an tsaro baki ɗaya. A halin yanzu, an kama sama da mutum 300, yawancinsu na hannunmu. Mun samu muggan makamai, mun kama da kwayoyi, buhunan wiwi, har da bindiga."
Kwamishinan yan sandan Kano
Lamarin daba ya yi kamari a jihohin Kano, Kaduna da Gombe Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Ya tabbatar da cewa wasu daga cikin waɗanda aka kama na zaune a gidan yari, yayin da wasu kuma ke tsare a hannun jami'an tsaro. Kan zargin cewa wasu 'yan siyasa na hana ruwa gudu wajen yaki da daba, DSP Mansir ya ce, a matakin rundunar 'yan sanda, za su ci gaba da kokarin hana laifi tare da kama masu aikata su.

Matakan hana ƙwacen waya a jihar Gombe

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta fitar da hana ɗaukar makamai wuraren taro da bukukuwa, tare da kakabawa masu babura wasu sharadin daina yawo da mutum biyu. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a shafinsa na Facebook, an bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin hana tashe-tashen hankula da ayyukan Kalare a jihar.

Sanarwa ta kara da cewa:

"An hana bayyana da/ko ɗaukar makamai irin su wuka, adduna, gatari, sanduna da makamantansu a yayin shagulgula, bukukuwa ko kowanne taro a bainar jama'a."
"An haramta hawan babur daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe. Ba a yarda mutum ya ɗauki fiye da fasinja ɗaya a babur ba."

Kwacen waya ya haifar da fargaba a Kano

A wani labarin, kun ji cewa mazauna sassa daban-daban a jihar Kano sun bayyana fargaba a kan yadda matsalar daba da kwacen waya ya zama ruwan dare, inda ake kashe jama'a babu tausayi.

Rahotanni sun bayyana cewa daga bukukuwan Sallah babba, zuwa yanzu, an yi nasarar cafke wasu daga cikin masu tare bayin Allah, suna nuna masu miyagun makamai da illata jama'a.

Sai dai abin takaicin da ya afku a Unguwar Sheka, shi ne yadda gungun 'yan daba suka fito aiki, tare da hallaka matasa biyu a dare guda, sannan suka yi awon gaba da wayoyinsu na hannu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.