Tinubu, Gwamnonin Kaduna da Filato Sun Gana bayan Kisan Mutum 13 a Mangu

Tinubu, Gwamnonin Kaduna da Filato Sun Gana bayan Kisan Mutum 13 a Mangu

  • Gwamnan Kaduna ya fusata kan kisan matafiya a Filato, inda ya ce ba zai zuba ido ana kashe mutanen haka kawai ba
  • Harin da aka kai kan matafiya a Mangu na jihar Filato ya hallaka mutum akalla 13 a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure
  • Gwamnatin Filato ta ce an an cafke wasu mutum 20 da ake zargi, amma gwamna Uba Sani ya bukaci a fadada bincike

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kanduna – Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na ganin an yi adalci ga matafiyanta da aka kashe a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato a ranar Asabar.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana harin a matsayin ta'addanci kuma ya yi Allah wadai da kisan, inda ya tabbatar da cewa ya tattauna da Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.

Gwamnan Kaduna ya yi tir da kusan matafiya 13 daga jiharsa
Gwamnan Kaduna ya gana da Tinubu, Muftwang kan kisan mutum 13 Hoto: Uba Sani/Caleb Muftwang
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnan ya bukaci Gwamna Caleb Muftwang da jami'an tsaro su tabbatar da an yi adalci ga bayin Allah da aka yiwa kisan gilla a jiharsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gana tsakanin gwamnan Filato da Kaduna

BBC Hausa ta ruwaito mutum 12 daga cikin matafiyan da suka fito daga Kaduna aka kashe yayin da suke tafiya domin halartar ɗaurin aure a cikin wata motar haya mallakin Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.

Rahotanni sun kara da cewa zuwa yanzu, adadin waɗanda suka rasu ya karu zuwa 13, yayin da wasu 16 daga cikin mutum 31 da ke cikin motar, na jinya a asibiti sakamakon harin.

Gwamna Uba Sani ya tabbatar da ya tattauna da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, domin nuna rashin jin daɗin abin da ya faru da kuma bukatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ya ce:

“Na kira Gwamnan jihar Filato, na kuma nuna masa cewa wannan mugun aiki da aka yi wa muatnenmu, ba za mu amince da shi ba."

Gwamnan Kaduna ya gana da Bola Tinubu

Gwamnan ya kuma ce ya tattauna da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da Babban Hafsan Tsaro Janar Christopher Musa, da kuma mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Gwamnan Kaduna ya ce za su bi hakkin mutum 13 da aka kashe a Filato Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Ya ce an yi tattaunawar don tabbatar da cewa gwamnati ta bi diddigin lamarin, domin babu dalilin da zai sa matafiya marasa laifi su shiga hannun mutanen da ba su da imani da sanin darajar rayuwa.

Ya ce gwamnatin Filato ta cafke mutum 22 da ake zargi da hannu a kisan, amma ya bukaci a fadada binciken domin gano masu hannu a cikin lamarin tare da gurfanar da su gaban kotu.

Gwamnan ya ce:

“Na kuma shaida wa shugaban ƙasa cewa zan yi tsayin daka a matsayina na gwamna domin ganin waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki sun fuskanci hukunci."

Martanin gwamnan Kaduna kan kashe mutanensa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya 'yan asalin jiharsa a Mangu ta jihar Filato.

Gwamnan ya ce mutum 12 da suka fito daga jihar Kaduna ne aka kashe a harin yayin da suke kan hanyarsu zuwa karamar hukumar Qua’an Pan domin halartar ɗaurin aure.

Tuni aka samu karuwar adadin mutanen da suka rasa rayukansu a mummunan harin ya faru ne a yankin Mangun da ke fama da rikice-rikice a 'yan kwanakin nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.