Ganduje Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Daliin da Ya Sa Ake Yawan Samun Mabarata a Arewa
- Ana yawan korafi kan yadda mabarata ke yawo a tituna na manyan biranen Arewacin Najeriya domin yin bara
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa akwai dalilin da ya sanya matsalar ke yawa aukuwa
- Abdullahi Umar Ganduje ya an dade ana nuna wariya ga nakasassu a Arewacin Najeriya, wanda hakan ya jefa da yawa daga cikinsu cikin harkar bara
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan matsalar bara a Arewa.
Ganduje ya danganta ƙaruwar mabarata Arewacin Najeriya da abin da ya bayyana a matsayin “daɗaɗɗen sakaci” da aka yi wa nakasassu a yankin.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Afirilun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Daga fitowa motsa jiki, tsohon 'dan wasan Najeriya ya rasu a Kaduna
Ganduje ya halarci taro
Ganduje ya yi jawabin lokacin bikin nuna fim ɗin tarihin cika shekaru 10 na kafuwar ƙungiyar Let’s Talk Humanity, wata ƙungiya da ke mayar da hankali kan inganta hanyoyin samun ilimi ga kurame da makafi.
Taron ya haɗa masu ruwa da tsaki a fannin ilimin nakasassu, jami’an gwamnati, da ɗaliban da suka amfana da makaranta ta musamman ta Tudun Maliki, domin murnar shekaru 10 ana fafutukar tabbatar da ilimi ga kowa.
Me Ganduje ya ce kan yawaitar mabarata?
Ya nuna takaicinsa kan abin da ya siffanta da wariya da ake yi wa nakasassu a Arewa, inda ya ce wannan yanayin ya taimaka wajen yawaitar mabarata a manyan birane.
“A Arewa, nakasassu mutane ne da aka mayar da su saniyar ware. Gani ya kori ji, babu shakka. Shi ya sa muke da jerin mabarata a sassan Arewacin wannan ƙasar rana da dare. Wasu suna kwana a ƙarƙashin gadoji, wasu kaɗan kuma a gefen titi. Wannan abin tausayi ne."
- Abdullahi Umar Ganduje
Sai dai, Ganduje ya ce wannan shiri da aka baje koli a wurin taron ya nuna cewa akwai damar samun canji idan gwamnatoci da masu ruwa da tsaki suka rungume shi, jaridar Leadership ta kawo rahoton.
“Amma idan aka kalli abin da muke da shi a nan yau, za ku ga cewa akwai wani gagarumin canji da ke gudana. Idan har abin da muke gani gwamnoninmu da hukumomin da abin ya shafa za su iya ɗauka, babu shakka za a samu babban canji mai kyau a cikin al’ummarmu."
- Abdullahi Umar Ganduje

Source: Facebook
Ya koka kan watsi da nakasassu a Arewa
Ya lura cewa wariyar ta shafi kwarin gwiwa da burin nakasassu da dama, amma ya ce shiga tsakani ta hanyar shirye-shirye na musamman na iya dawo masu da martabarsu da kuma sa su zama masu amfani ga kansu.
“Haka ne, an mayar da su baya saboda naƙasarsu ta jiki. Wannan ya shafi tunaninsu da kwarin gwiwarsu. Ba sa ma iya tunanin kansu a matsayin mutane kamar kowa."

Kara karanta wannan
2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar
"Sai dai, ta hanyar bayyana irin waɗannan shirye-shiryen, muna koya masu yadda za su zama kamar kowane ɗan adam na gari a cikin al’ummarmu."
- Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya gina masallaci a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon masallacin da gidauniyarsa ta gina a jihar Kano.
Mai martaba sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci bude sabon babban masallacin Juma'a da aka gina.
Rahotanni sun nuna cewa gidauniyar raya addinin Musulunci ta Ganduje ce ta dauki nauyin ginin masallacin karkashin jagorancin, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Legit.ng
