Shirin Dawowa Yaki: Iran za Ta kai Dogayen Hare Hare kan Amurka
- Dakarun kasar Iran sun yi gargadi da cewa za su kai manyan hare-hare mazu zafi kan kadarorin Amurka idan aka sake tabo su da yaki
- Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da takaddama tsakanin Amurka da Iran kan bude mashigar Hormuz bayan tsayar da yakin da suka yi
- Jagora addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa kasashen da ba su yankin Gabas ta Tsakiya ba su da ta cewa kan Hormuz
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Kasar Iran ta yi gargadin cewa za ta kaddamar da dogayen hare-hare masu raɗaɗi kan kadarorin Amurka idan Washington ta sake far mata da yaki.
Hakan na zuwa ne yayin da rikici ke ci gaba kan rufe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta yi da kuma tangardar kokarin kawo karshen rikicin gaba daya.

Kara karanta wannan
Khamenei ya fusata game da barazanar Amurka, ya fadi shirin Iran kan makamin nukiliya

Source: Getty Images
Rahoton Indian Express ya nuna cewa Iran ta yi gargadin ne a daidai lokacin da za a yi wa Donald Trump bayani kan matakin da ya kamata ya dauka kan Tehran.
Gargadin Iran ga kasar Amurka
Wani babban jami’i a rundunar sojin Iran ya ce duk wani sabon hari daga Amurka, ko da kuwa karami ne, zai janyo martani mai tsawo.
“Duk wani sabon hari da aka kawo mana, za a mayar da martani da dogayen hare-hare masu raɗaɗi,”
In ji jami’in.
Shugaban rundunar sararin samaniya, Manjo Janar Majid Mousavi, ya kuma yi gargadin cewa jiragen ruwan yakin Amurka na iya zama abubuwan da za a kai wa farmaki.
“Mun ga abin da ya faru da sansanoninku a yankin; hakan na iya faruwa da jiragen ruwanku,”
In ji shi.
Reuters ta ruwaito cewa an kunna tsarin kariya daga hare-haren sama a wasu sassan Tehran a daren Alhamis, inda kafafen yada labaran Iran suka ce sun yi mu’amala da jiragen sama marasa matuka da kuma jiragen leƙen asiri.
Bayanin Khamenei kan Hormuz
Mashigar Hormuz na ci gaba da kasancewa muhimmin bangare na wannan rikici. Iran ta nuna cewa za ta ci gaba da rike ikon sarrafa mashigar karkashin abin da ta kira “sabon tsari”.
Jagoran koli, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya ce ba a maraba da dakarun kasashen waje a yankin:
“Baƙin da suka zo daga nesa dubban kilomita ba su da ta cewa,”

Source: Getty Images
A yanzu haka dai rikicin ya riga ya shafi kasuwannin duniya. Farashin danyen mai na Brent ya taba haura dala 126 a kowace ganga kafin ya sauka zuwa kusan dala 114.
Trump ya yi wa Iran barazana
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka ya yi wa kasar Iran sabuwar barazana yana nema ta mika wuya gaba daya bayan yakin da suka yi.
Donald Trump ya bayyana a wani hoto dauke da babbar bindiga a wani waje da ke da abubuwan fashewa ya sanya bakin tabarau yana nuna cewa da gaske yake.
A sakon da ya wallafa a hade da hoton, shugaba Trump ya bayyana cewa babu sassauci a duk wata alaka da zai yi da Iran a kwanaki masu zuwa.
Asali: Legit.ng
