Gwamnan Binuwai Ya Dakatar da Hadiminsa da ake Zargi da Tilasta wa Mata Lalata da Shi
- Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya dakatar da Mkor Aondona daga mukaminsa na Mai ba da shawara na musamman
- Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce an dakatar da Aondona har sai baba ta gani bisa zargin yana yiwa mata dole su yi lalata da shi
- Gwamnatin ta kara da cewa ba za ta zuba idanu ba, wasu daga cikin jami'anta na amfani da mulki wajen tozarta jama'a ba, musamman mata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Benue – Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya dakatar da Mista Mkor Aondona daga matsayin mai ba shi shawara na musamman kan shirye-shirye, bincike da tsara tsare-tsare.
Wannan ya biyo bayan kamen da jami’an Hukumar EFCC suka yi masa bisa zargin tilastawa mata yin lalata da shi da barazanar yaɗa sirrinsu ta kafar intanet.

Asali: Facebook
Sanarwar da gwamnati ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce gwamnan ya dauki matakin ne a matsayin wani bangare na cika alkawurransa na jajircewa wajen kare mutunci da gaskiya a cikin aikin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar Binuwai ya gargadi jami'anta
Gwamna Alia ya bayyana cewa kowane jami’in gwamnatinsa da aka kama da laifi ko sabawa dokokin aiki zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa doka za ta yi aikinta ba tare da katsalandan ba ko nuna son kai domin a tabbatar da adalci.
Haka kuma ya kare tare da jan kunne cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da duk wani abu da zai bata sunanta ko kuma ya hana jama’a yarda da ita ba.

Asali: Twitter
Gwamnan ya nanata cewa kujerar mulki wata dama ce ta yi wa jama’a hidima da gaskiya, kuma duk wanda ya kauce wa wannan hanya ba shi da gurbin zama a cikin gwamnatinsa.
An ba hadimin gwamnan Binuwai umarni
A cewar sanarwar wacce sakataren yada labaran gwamna, Tersoo Kula ya sanya wa hannu, an umurci hadimin da aka dakatar da ya mika kansa ga hukumomin.
Gwamnatin ta ce wannan zai bayar da dama ya fuskanci dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa na tilasta wa mata lalata da shi.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnatin Jihar Binuwai a karkashin Rev. Fr. Hyacinth Alia na ci gaba da jajircewa wajen kare haƙƙi da mutuncin 'yan jihar, musamman mata da ƙungiyoyin marasa ƙarfi, tare da yin aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da adalci."
Binuwai: An kashe jagora a jam'iyyar PDP
A baya, mun wallafa cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe tsohon shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Tarka a jihar Binuwai, Aondoakaa Yaiyol.
Rahotanni sun bayyana cewa kafin kisan nasa, Aondoakaa Yaiyol shi ne kwamandan rundunar mafarauta da masu samar da tsaro a jeji (NHFSS) da ke yankin.
Sakataren yaɗa labarai na PDP a jihar, Tim Nyior, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana kisan a matsayin abin takaici matuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng