'Yan Sanda Sun Cafke Mutanen da Ake Zargi kan Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau

'Yan Sanda Sun Cafke Mutanen da Ake Zargi kan Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau

  • Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta cafke wasu daga cikin mutanen da ake zargi kan kisan ƴan ɗaurin aure da suka taso daga Kaduna
  • Kakakin ƴan sandan jihar ya bayyana cewa an cafke mutum 22 da ake zargin akwai hannunsu a cikin aika-aikar
  • Hakazalika ya ƙara da cewa an garzaya da mutanen da suka jikkata sakamakon harin zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta bayyana cewa ta cafke wasu da ake zargi kan kisan masu zuwa ɗaurin aure daga Kaduna.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa ta cafke mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan ƴan ɗaurin aure 12 a jihar.

'Yan sanda sun kama masu laifi a Plateau
'Yan sanda sun cafke mutanen da ake zargi a Plateau Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar TheCable ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe ƴan ɗaurin aure a Plateau

A ranar Juma’a, wasu mutane 12 sun rasa rayukansu bayan da wasu gungun matasa suka ƙona motar da ke ɗauke da matafiya daga Zariya, jihar Kaduna zuwa ƙaramar hukumar Quan Pan da ke Plateau domin halartar ɗaurin aure.

Wasu daga cikin matafiyan sun samu raunuka daban-daban a sakamakon harin.

Rahotanni sun ce matafiyan sun yi ɓatan hanya ne kafin a rutsa da su a yankin Mangu, inda wasu suka kai musu hari.

A cikin sanarwar da Alfred Alabo, ya fitar, ya bayyana cewa mutane 21 daga cikin matafiyan an ceto su kuma an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Bayan samun rahoton, kwamishinan ƴan sanda na jihar Plateau ya gaggauta umartar DPO na Mangu da ya tattara jami’ansa tare da garzayawa wurin da lamarin ya faru."
“Da isarsu wurin, jami’anmu tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun tarwatsa fusatattun gungun jama’ar, suka kuma ceto mutum 21, inda aka garzaya da su asibiti domin yin jinya."

"Binciken farko da muka gudanar ya nuna cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su masu zuwa biki ne daga Zariya, jihar Kaduna, da suke kan hanyarsu ta zuwa Quan Pan domin halartar ɗaurin aure, amma suka yi ɓatan hanya."
"Fusatattun mutanen sun tare motar da suke ciki sannan suka ƙona ta. A sakamakon haka, wasu daga cikin fasinjojin sun rasa rayukansu, yayin da mutum bakwai suka ji raunuka iri-iri."
“A cikin ƙarfin hali da kishin aiki, jami’anmu tare da sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar ceto mutum 14 ba tare da wani rauni ba."
“A karshe, mun kama mutum 22 da ake zargi da hannu a wannan lamari."

- DSP Alabo Alfred

Matasa sun kashe 'yan daurin aure a Plateau
An kashe 'yan daurin aure a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tinubu ya yi Allah wadai kan kisan ƴan ɗaurin aure

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya nuna takaicinsa kan kisan kiyashin da aka yi wa masu zuwa ɗaurin aure a jihar Plateau.

Mai girma Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan inda ya bayyana shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

Shugaban ƙasan ya kuma umarci jami'an tsaro kan su tabbatar sun zaƙulo masu hannu a cikin mummunan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng