Watanni 2 da Kisan Hausawa a Uromi, Kano da Edo Sun Gaza Cimma Matsayar Diyya

Watanni 2 da Kisan Hausawa a Uromi, Kano da Edo Sun Gaza Cimma Matsayar Diyya

  • Rahotanni sun bayyana cewa har yanzu iyalan mafarautan Kano 16 da aka hallaka a garin Uromi na jihar Edo ba su ji bayani kan diyya ba
  • A ranar 27 ga Maris, 2025, wasu matasa 16 ‘yan farauta daga Kano sun gamu da ajalinsu yayin da bata-garin 'yan Uromi suka tare su a hanya
  • Majiyoyi sun bayyana cewa tuni gwamnatin jihar Kano ta mika bukatunta da tayin diyya ga gwamnan Edo, Monday Okpebholo, amma har yanzu shiru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fiye da watanni biyu kenan da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattauna batun diyya da iyalan mafarautu 16 da aka kashe a garin Uromi.

Gwamnatocin jihohin Edo da Kano sun yi alkawarin za su dauki matakan tabbatar da an biya diyya ga iyalan Hausawan da wasu 'yan Uromi su ka yi wa kisan wulakanci a jiharsu.

An kashe Hausawa 16 a Uromi
Har yanzu iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi ba su ji komai ba Hoto: Sam digitalz/Fahd Muhammad
Asali: Facebook

A wani labari da ya kebanta ga jaridar Punch, gwamnatin Kano ta kafa kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dora wa kwamitin alhakin tattaunawa da Gwamnatin Jihar Edo domin fitar da adadin diyya da iyalan mutane 16 za su samu

Babu matsaya tsakanin gwamnatcin Kano da Edo

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa tattaunawar na iya fuskantar cikas sakamakon sabani da aka samu dangane da adadin diyya da ya kamata a biya iyalan.

Wata majiya mai tushe da ke da masaniya kan al’amarin, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar cewa an samu sabani a kan abin da ya kamata a biya iyalan.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta mika bukatar diyya ga gwamnan Edo Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Majiyar ta ce:

“Dalilin da ya sa kwamitin bai fito ya ce komai ba shi ne saboda akwai rashin jituwa tsakanin jihohin biyu kan abin da ya kamata a biya.”

Sai dai Gwamnatin Kano ta ƙi yin tsokaci a hukumance game da batun duk da kokarin tuntubar Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Waiya.

Kano: An mika bukata ga gwamnan Edo

Wani jami’i daga Gwamnatin Jihar Edo, wanda shima ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa tawagar Kano ta riga ta mika tayin diyya ga Gwamna Monday Okpebholo.

Majiyar ta ce gwamnan ne kaɗai zai iya yanke hukunci ko ya bayyana matsayar jiharsa a kan bukatar da aka mika mata.

Majiyar ta ce:

“Abin da zan iya cewa a yanzu shi ne an riga an mika tayin daga Gwamnatin Kano ga gwamnanmu. Sai shi ne kawai zai iya yanke hukunci ko ya bayyana yadda gwamnati ke kallon lamarin.”

A ranar 27 ga Maris, 2025, wasu matasa 16 ‘yan farauta daga Kano suka gamu da ajalinsu bayan wasu mazauna garin Uromi a Jihar Edo sun tare su, tare da yi masu kisan gilla.

Iyalan mafarautan jihar Kano sun ji shiru

A wani labarin, kun ji cewa Iyalan mafarautan jihar Kano da aka kashe a garin Uromi da ke Jihar Edo sun sake neman gwamnatin tarayya da ta tabbatar da adalci ga 'yan uwansu da aka hallaka.

Mafarautan 16 da aka kashe sun fito ne daga ƙananan hukumomin Kibiya, Rano da Bunkure na Jihar Kano, kuma an kashe su ne a lokacin da suke cikin tafiya daga Fatakwal zuwa Kano.

A lokacin sadakar kwanaki 40 da aka yi wa mamatan a sakatariyar ƙaramar hukumar Kibiya, dangi, abokan arziki da mazauna yankin sun gudanar da addu’o’i na neman rahamar Allah gare su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.