Tsohon Gwamnan Bauchi Ya Tara Shettima, Atiku, Kwankwaso, El Rufa'i a Abuja
- Tsofaffin shugabanni da jiga-jigan siyasa sun taru domin taya tsohon gwamnan Bauchi, Ahmadu Adamu Mu’azu, murnar zagayowar ranar haihuwarsa
- Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya wakilci shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen taron da ya tara Olusegun Obasanjo da Yakubu Gowon
- Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar da Bala Mohammed sun yaba da irin gudunmuwar Mu’azu a ci gaban jihar Bauchi da Najeriya gaba ɗaya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugabanni da dama daga ɓangarori daban-daban na Najeriya sun halarci taron taya tsohon gwamnan Bauchi, Ahmadu Adamu Mu'azu murnar cika shekara 70.
Rahotanni sun nuna cewa Ahmadu Adamu Mu'azu ya shugabanci jam’iyyar PDP a matakin ƙasa a shekarun baya.

Asali: Facebook
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jero manyan Najeriya da suka halarci taron a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wadanda suka halarci taron akwai tsofaffin shugabannin ƙasa, Olusegun Obasanjo da Yakubu Gowon.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i, Danjuma Goje da sauran fitattun ‘yan siyasa sun halarci taron.
Yayin da ya yaba da kokarin da tsohon gwamnan ya yi, Sanata Kashim Shettima ya wallafa a X cewa ya wakilci Bola Tinubu ne a wajen taron.
Rabiu Kwankwaso ya taya Adamu Mu'azu murna
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana farin cikinsa bisa kasancewa cikin manyan shugabannin da suka halarci bikin taya Mu’azu murna.
Ya ce:
“Na ji daɗin kasancewa tare da shugabanni irinsu Olusegun Obasanjo, Yakubu Gowon, Kashim Shettima, da Atiku Abubakar wajen taya abokina Alhaji Ahmadu Adamu Muazu murnar cika shekara 70.
Bala Mohammed ya yabawa Adamu Mu'azu
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana Mu’azu a matsayin zakaran da ya kawo sauyi a jihar, yana mai cewa gwamnatinsa da al’ummar Bauchi na alfahari da ayyukansa.
A sakon da ya wallafa a Facebook, gwamnan ya ce:
“Madalla da cikar ka shekara 70, Walin Bauchi. Mun yaba da jajircewarka a matsayin tsohon gwamna da kuma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa.
"Jagorancinka ya haifar da sauyi, da burin ganin Najeriya ta zauna lafiya kuma ta ci gaba.”
Gwamna Bala ya roki Allah da ya ci gaba da ba Mu’azu lafiya da hikima, yana mai cewa irin rawar da ya taka a Najeriya abin koyi ne ga masu rike da madafun iko a yau.

Asali: Facebook
Atiku ya tuna da shekarun aiki da Adamu Mu'azu
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa lokacin da yake aiki da Mu’azu daga 1999 zuwa 2007, sun yi aiki tare wajen gina tubalin shugabanci nagari.
Atiku ya wallafa a Facebook cewa:
“Na kasance tare da ubangidana Obasanjo da sauran shugabanni wajen nuna girmamawa ga Mu’azu.
"Yana da babban tarihi a siyasa da jagoranci. Ina fatan Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.”
Ya ƙara da cewa irin gudunmuwar Mu’azu a matsayin gwamna da shugaban jam’iyya ta taimaka wajen inganta tsarin mulki da haɓaka ci gaban Najeriya.
Keyamo ya soki Atiku da El-Rufa'i kan ADA
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan sufurin jiragen sama, Festus Kiyamo ya soki Atiku Abubakar da sauran 'yan adawa kan kafa ADA.
Keyamo ya ce kokarin da Nasir El-Rufa'i da wasu 'yan siyasa suka fara na ganin sun yi wa Bola Tinubu taron dangi ba zai yi nasara ba.
Martanin Keyamo ya samo asali ne bayan manyan 'yan siyasa daga bangaren adawa sun tura bukatar kafa jam'iyyar ADA domin karawa da APC a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng