Sule Lamido Ya Tayar da Kura bayan Zargin Tinubu da Mahaifiyarsa da Rusa Zaben Abiola

Sule Lamido Ya Tayar da Kura bayan Zargin Tinubu da Mahaifiyarsa da Rusa Zaben Abiola

  • Fadar shugaban ƙasa ta karyata zargin Sule Lamido na cewa Bola Tinubu da mahaifiyarsa sun mara wa soke zaben 12 ga Yunin 1993 baya
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu ya kasance jagora a fafutukar dawo da dimokuraɗiyya bayan soke zaben
  • An zargi Lamido da kasancewa cikin shugabannin jam’iyyar SDP da suka kasa kare nasarar MKO Abiola a 1993 bayan rusa zaben da aka yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta yi martani a hukumance kan wasu kalaman tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ga Bola Tinubu.

Sule Lamido ya zargi Bola Tinubu da hannu wajen ruguza zaben da aka yi a lokacin gwamnatin Janar Ibrahim Babangida.

Fadar shugaban kasa ta wanke Tinubu daga zargin Sule Lamido
Fadar shugaban kasa ta wanke Tinubu daga zargin Sule Lamido. Hoto: Sule Lamido|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Legit ta gano cewa fadar shugaban kasa ta karyata maganar da Sule Lamido a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana kalaman Lamido a matsayin ƙarya da ƙoƙarin sake fasalta tarihi ta hanyar ɓoye gaskiya.

Sule Lamido: Fadar shugaban kasa ta wanke Tinubu

Onanuga ya ce ba wai Tinubu ya tsaya tare da MKO Abiola ba ne kawai, har ma ya kasance cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar NADECO da ta jagoranci yaki da gwamnatin soja bayan soke zaben.

Fadar shugaban ƙasa ta ce hotuna da bayanai na tarihi sun tabbatar da kasancewar Tinubu a cikin waɗanda suka taka baya ga Abiola wajen fafutuka.

A martanin da ta yi, fadar shugaban kasa ta ce saboda kokarin da Tinubu ya yi, an kama shi tare da wasu ‘yan majalisa aka tsare su a Alagbon, bayan rusa majalisar.

An zargi Sule Lamido da gaza kare SDP

Sanarwar ta zargi Lamido, wanda a wancan lokaci shi ne sakataren SDP, da kasancewa cikin shugabannin jam’iyyar da suka amince da gwamnatin wucin gadi bayan Babangida ya sauka.

Tashar Arise News ta wallafa cewa Onanuga ya ce:

“Lamido da Tony Anenih sun sayar da nasarar da MKO Abiola ya samu wajen aiki tare da jam’iyyar da ta sha kaye domin hana Abiola mulki.”

Ya ce sabanin Lamido, Tinubu ya tsaya tsayin daka wajen kare zaben tare da tallafa wa masu zanga-zanga, ciki har da toshe gadar Third Mainland a Legas.

Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya taka rawa a dawo da dimokuradiyya.
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya taka rawa a dawo da dimokuradiyya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Sunday Dare ya caccaki Sule Lamido

Wani hadimi ga Shugaba Tinubu, Sunday Dare, ya bayyana cewa Lamido yana buƙatar warkewa daga rudanin da ya shiga.

Dare ya wallafa a X cewa:

“Na san da rawar da Tinubu ya taka a wancan lokaci. Shi ne jagoran fafutukar dawo da dimokuraɗiyya. Sai Lamido ya fadi rawar da shi ya taka.”

Lamido ya zargi Tinubu da juya tarihi

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya zargi Bola Tinubu da kokarin rikita tarihin Najeriya.

Sule Lamido ya yi magana ne bayan wani jawabi da Bola Tinubu ya yi a zauren majalisar tarayya a ranar dimokuradiyya.

Lamido ya ce Bola Tinubu ya fadi wasu abubuwan da ba haka suke ba da kuma karrama mutanen da ba su dace ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng