Adamu Mu’azu yayi raddi ga Goodluck Jonathan
-Adamu Mu’azu yayi raddi gameda zargin da ake masa
-Yace yayi iyakan kokarinsa wajen tabbatar da cewa Jonathan yaci zaben 2015
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP. Adamu Ahmed Muazu ya mayar da martani ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, akan zargin da ya masa cewa yana daga cikin wadanda suka yaudaresa a zaben 2015 da ya gabata.
Ya bayyana wannan ne ta shafinsa na Facebook inda yace:
“Banyi niyyar mayar da martani akan zargin akayi mini na cewa na yaudari shugaba Jonathan da jam’iyyata ba, amma na lura cewa shiru akan hakan zai iya sa mutane tunanin hakan ya faru.
Na matukar mamakin cewa shugaba Jonathan zai yi mini irin wannan zargi. Shin ta yay azan yaudari kaina?.
A lokacin da nike shugaba jam’iyyar PDP, na kasance kan gaba wajen yakin neman zabe. Wadanda suke zargin cewa na yaudari Jonathan da jam’iyyata basu son gaskiya.
Yayinda muke shan zage-zage daga yan uwanmu da abokanmu, mun goyi bayan Jonathan da gaske.
KU KARANTA:
Maganar gaskiya shine, nayi iyakan kokarina ga jam’iyyata. Wadanda suke ganin laifinmu ne rashin samun kuri’un jihohin arewa sun manta cewa mutane ke zabe.”
A wata littafin a aka rubuta, shugaba Goodluck Jonathan ya lissafa tsohon shugaban jam’iyyar PDP a matsayin wadanda suka yaudaresa ya fadi zaben.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng