2027: Gwamnoni 4 da Ƴan Majalisa da Ake Zargin Suna Harin Kujerar Kashim Shettima
- Ana rade-radin cewa APC na kokarin cire Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima daga tikitin 2027, saboda rikice-rikicen siyasa daga jihar sa
- Gwamnoni hudu daga Arewa da manyan 'yan majalisa biyu suna zawarcin kujerar mataimakin shugaban kasa
- Wasu sun ce Shettima bai samu cikakken amincewa daga Shugaba Tinubu ba, duk da cewa suna yawan ganawa da juna a Fadar Shugaban Kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Makomar siyasar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima na cikin hadari, yayin da wasu alamu daga cikin jam’iyyar APC ke nuna zai rasa tikitin 2027.
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa da APC sun shaida cewa ana wasu lissafe-lissafen siyasa da ka iya sa Tinubu sauya mataimaki.

Asali: Twitter
Ana hasashen sauya Shettima daga mukaminsa
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu gwamnoni hudu daga Arewa da manyan 'yan majalisa biyu ke harin kujerar mataimakin shugaban kasa, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wata majiya, makarkashiyar na da nasaba da sukar gwamnatin Tinubu da Gwamna Babagana Zulum na Borno da Sanata Ali Ndume ke yi a fili.
Majiya ta ce:
“Babban matsalar Shettima ita ce halayen ‘yan siyasar jiharsa, ciki har da gwamna da Ndume, da ke sukar gwamnati a fili.
“Idan gwamna da sanata daga jiharka, musamman wanda ka damka masa mulki na sukar gwamnati, hakan yana haifar da matsala.”
Zargin Wasu sun fara neman kujerar Shettima
Bayan rikicin taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas, an gano cewa wasu sun fara shirya kansu don samun kujerar mataimaki.
Wani jigo ya ce:
“Zai iya yiwuwa domin Shettima ba shi da kusanci sosai da Shugaba, ba a ce za a canza shi ba, amma ba a tabbatar ba.
“Amma hakan bai hana wasu shirya kansu ba, don kada ace idan shugaban ya sauya shawara ko kuma ya yanke hukunci daban.”

Asali: Twitter
Gwamnonin da ake zargin na son kujerar Shettima
Wata majiya ta kara da cewa, jiga-jigai biyu na majalisa da gwamnoni hudu suna da hannu, biyu daga Arewa maso Gabas da biyu daga Arewa maso Yamma.
Gwamnonin da ake tunanin za su maye gurbin Shettima sun hada da na Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya.
Sai kuma gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da kuma takwaransa na jihar Katsina, Dikko Umaru Radda.
Shugabannin majalisar tarayya da aka kira sunayensu
Majiyoyi sun kuma ambaci Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abass da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, a matsayin masu zawarcin kujera.
“Yawanci gwamnoni ne ke son wannan kujera sun hada da gwamnan Yobe, Gombe, Kaduna da Katsina duk ana zargin suna da muradi.
“Muna kuma ganin alamun cewa Kakakin Majalisa da Barau Jibrin na sha’awar kujera, dukkaninsu na wakiltar bangarori daban-daban na siyasa."
- Cewar wata majiya
Fadar shugaban kasa ta magantu kan kujerar Shettima
Kun ji cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ba zai bayyana wanda zai kasance mataimakinsa a 2027 ba a yanzu.
Hadiminsa shugaban kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce yin hakan yana cikin tsarin mulki, kuma babu matsala tsakanin Tinubu da Kashim Shettima.
Bayo Onanuga ya ce jita-jitar cewa za a ajiye Sanata Kashim Shettima sun samo asali ne daga zato da maganganu marasa tushe balle makama.
Asali: Legit.ng