Yanzu yanzu: Ahmad Muazu ya saka labule da Osinbajo a Abuja

Yanzu yanzu: Ahmad Muazu ya saka labule da Osinbajo a Abuja

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Adamu Muazu na kan wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa, Abuja. Sai dai har yanzu ba a bayyana dalilin wannan ganawar ba.

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga jaridar Daily Trust, na nuni dacewa, an fara gudanar da wani zaman sirri tsakanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Adamu Muazu a cikin fadar shugaban kasa Abuja.

Muazu, wanda kuma ya taba zama gwamnan jihar Bauchi har na tsawon shekaru 8, ya isa sashen mataimakin shugaban kasar ne da misalin karfe 4 na yamma, kuma kai tsaye ya shiga ganawar sirrin da Farfesa Osinbajo.

KARANTA WANNAN: Tazarcen Buhari: Manoma miliyan 12 sun fara yin karo karon N100 don yakin zaben APC 2019

Yanzu yanzu: Ahmad Muazu ya saka labule da Osinbajo a Abuja

Yanzu yanzu: Ahmad Muazu ya saka labule da Osinbajo a Abuja
Source: UGC

Sai dai wakilin jaridar bai samu damar tattara rahoto kan ko akwai hadin wannan ganawar da yunkurin Muazu na sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC ba.

Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa wannan ganawar ta biyo mako daya da ganawar mataimakin shuagabn kasar da wani tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, wanda ya sauya sheka zuwa APC.

Muazu, wanda yake buga kirji da sunan 'Game Changer', ya jagoranci jam'iyyar PDP wajen shan kaye a zaben 2015 a kasar, wanda ya kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel