2027: Masu Hadakar Kafa ADA Sun Samu Kalubalen Farko daga Ministan Tinubu
- Festus Keyamo SAN ya ce babu wata hadakar jam’iyyu da ke cikin yunkurin kafa jam’iyyar ADA da ake yayatawa
- Ya bayyana cewa kawai wasu 'yan Najeriya ne ke amfani da damar su ta kundin tsarin mulki don yin rajistar sabuwar jam’iyya
- Keyamo ya kwatanta wannan yunkuri da ƙoƙarin yaudarar al’umma da jefa su cikin rudani da ya ce ba shi da tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa ba wani hadin gwiwa na jam’iyyu da aka yi a yunkurin da wasu ke cewa suna son kafa jam’iyyar ADA.
Ya yi magana ne yayin da manyan 'yan adawan Najeriya suka zabi kafa jam'iyyar ADA domin kalubalantar APC a zaben 2027.

Asali: Facebook
A sakon da ya wallafa a X, Keyamo ya ce wannan yunkuri bai wuce ƙoƙarin wasu ‘yan ƙalilan ba na amfani da haƙƙinsu na yin rajistar jam’iyya, wanda ya ce ba sabon abu ba ne a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Keyamo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa wannan yunkuri yana ƙoƙarin jefa mutane cikin ruɗani da ƙirƙirar abubuwan da ba su wanzu ba.
Ana sa ran wasu 'yan adawa za su taru a jam’iyyar ADA domin kalubalantar APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Babu hadin gwiwar jam’iyyu inji Keyamo
Keyamo ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da aka sani da ta shiga cikin wannan sabon shiri na ADA.
Ya ce wannan ƙoƙari na ‘yan adawa bai kai matsayin hadakar jam’iyyu irin wanda ya samar da APC a shekarar 2013 ba.
Ministan ya ce:
“Wannan ba komai ba ne illa ƙoƙarin wasu mutane kalilan na yin rajista da INEC domin kafa sabuwar jam’iyya.
"Amma suna ƙoƙarin yaudarar mutane da cewa wata gagarumar ‘hadaka’ ce, alhali babu hakan a cikin tafiyar”
Ya ƙara da cewa ko shakka babu, wannan yunkuri na nuni da irin ruɗanin da ake ƙoƙarin yadawa a tsakanin ‘yan Najeriya da nufin samun farin jini a idon jama’a.
Keyamo ya ce ba irin hadakar APC ba ce
A cewar Keyamo, ba za a kwatanta wannan yunkuri da wanda ya haifar da jam’iyyar APC a shekarar 2013 ba.
Ya ce a 2013 jam’iyyu da dama ne suka haɗu suka kafa babbar jam'iyya da ta yi nasarar karɓar mulki daga PDP.

Asali: Facebook
Vanguard ta rahoto ya ce:
“Idan suna tunanin za su maimaita abin da APC ta yi a 2013, to wannan wani barkwanci ne kawai.
Tinubu zai dauki mataimaki a 2026
A wani labarin, mun rahoto muku cewa fadar shugaban kasa ta yi magana kan lokacin da Bola Tinubu zai sanar da mataimakin shi na 2027.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce sai bayan taron APC na 2026 Bola Tinubu zai fitar da sanarwa.
Hakan na zuwa ne bayan maganganu sun yawaita kan makomar mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng