An Kashe Hausawa Suna Tafiya Daurin Aure a Filato, Sojoji Sun kai Dauki

An Kashe Hausawa Suna Tafiya Daurin Aure a Filato, Sojoji Sun kai Dauki

  • Wasu matasa masu tayar da hankali sun kai hari kan fasinjoji a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, inda suka kashe mutum tare da jikkata wasu 21
  • Fasinjojin ‘yan kabilar Hausa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa bikin aure a Qua’an-Pan, amma sun bace suka shiga wani yanki na karamar hukumar Mangu
  • Cikin gaggawa, sojojin Najeriya karkashin Operation Lafiyan Jama’a suka kai dauki inda suka ceci rayuka da dama tare da kai wadanda suka jikkata asibiti

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Rundunar sojojin Najeriya ta hana afkuwar mummunar kisan kiyashi a jihar Filato, bayan da wasu matasa suka kai hari kan fasinjoji a yankin Mangu.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Mangu a ranar Juma’a, 20 ga Yuni, 2025.

Sojoji sun dakile faruwar mummunar kisan kai bayan kai hari wa matafiya a Filato
Sojoji sun dakile faruwar mummunar kisan kai bayan kai hari wa matafiya a Filato. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa fasinjojin ‘yan kabilar Hausa ne, suna kan hanyarsu ce ta zuwa bikin aure a Qua’an-Pan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mummunan lamarin ya faru ne bayan bas din su ta bace hanya ta shiga titin Panyam–Kerang–Mangun da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

An kashe masu zuwa aure a jihar Filato

Maimakon a taimaka wa fasinjojin da suka bata hanya, wasu matasa da ake zargin sun dauki zafin kabilanci suka kai musu hari.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutum bakwai nan take, yayin da wasu 21 suka samu rauni mai tsanani.

Bayan harin, maharan sun kone motar su gaba daya, lamarin da ya haifar da fargaba a yankin tare da barazana ga zaman lafiya.

Sojoji sun kai dauki cikin gaggawa

Sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Lafiyan Jama’a sun kai dauki cikin gaggawa domin hana cigaba da kashe-kashen da ka iya rikidewa zuwa mummunar fitina.

Bayanai sun nuna cewa sojojin sun yi aiki cikin gaggawa da hikima inda suka ceto wadanda suka tsira daga harin tare da kai su inda za a kula da su.

An ba wadanda suka jikkata agajin gaggawa kafin a garzaya da su zuwa Asibitin Gwamnati da ke Mangu domin samun cikakken kulawa.

Bincike ya nuna cewa ba ‘yan bindiga ba ne

Rahotanni daga jami’an tsaro sun nuna cewa fasinjojin ba ‘yan ta’adda ba ne ko masu wani makirci, sai dai masu son zuwa bikin aure ne da suka bata hanya.

Wannan ya kara tabbatar da cewa harin da aka kai musu ya samo asali ne daga zargi marar tushe da kuma rashin dogon tunani daga wadanda suka aikata laifin.

An bukaci daukar matakan tsaro bayan kai hari Filato
An bukaci daukar matakan tsaro bayan kai hari Filato. Hoto: Plateau State Government
Asali: Twitter

Bukatar samar da zaman lafiya a Filato

Al’ummar yankin na kara fuskantar barazanar rikice-rikicen kabilanci da na addini, wanda hakan ke bukatar matakin gaggawa daga hukumomi da shugabannin al’umma.

Masu sharhi sun bukaci gwamnati ta zurfafa hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da shugabannin gargajiya domin hana sake aukuwar irin wannan mummunar matsala.

An bukaci azumi domin kawo zaman lafiya

A wani rahoton, kun ji cewa wasu malaman cocin Katolika a jihar Enugu sun bukaci a yi azumi da addu'o'i.

Sun bukaci haka ne domin rokon Allah ya kawo sauki a kan kashe kashe da ake yi a jihohin Benue da Filato.

Baya ga haka, sun yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta daukar matakan da suka dace a kan matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng