Ahmad Lawan: Sanatan da Ya fi Kowa Daɗewa, Ya Shekara 27 a Majalisar Tarayya
- Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe ya shafe shekaru da dama yana jagorantar mazabarsa tun bayan dawowar dimukradiyya
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa dan majalisar ya shafe shekaru 27 kan kujerar wanda wasu yan mazabarsa ke yaba masa
- Sanatan ya fara daga Majalisar Wakilai kafin ya koma Majalisar Dattawa, daga bisani ya zama shugaban sanatoci a shekarar 2019
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dimukuraɗiyya a Najeriya ta shafe shekaru 27 tun daga 1999 zuwa yanzu wanda hakan ya kawo ci gaba a ƙasa.
Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe shi ne mafi dadewa a cikin ƴan majalisar dattawa a yanzu.

Source: Facebook
Mutum 2 da suka fi dadewa a Majalisar tarayya
Daily Trust ta rawaito cewa Sanata Ahmed Lawan da Nicholas Mutu su ne ‘yan majalisa mafi dadewa a Majalisar Tarayya tun shekarar 1999.
Dukkaninsu sun shiga Majalisar Wakilai bayan dawowar dimokuradiyya, kuma zuwa shekarar 2027 za su cika shekaru 28 suna majalisa ba tare da katsewa ba.
Ahmed Lawan ya wakilci mazabar Bade/Jakusko a Majalisar Wakilai daga 1999 zuwa 2007 kafin ya lashe kujerar Sanatan Yobe ta Arewa inda Mutu ke ci gaba da zama a majalisar wakilai.
Tun daga lokacin ya ci gaba da samun nasara a zabuka, inda daga baya ya zama Shugaban Majalisar Dattawa tsakanin shekarun 2019 zuwa 2023.
Kwamitocin majalisa da Ahmed Lawan ya jagoranta
Kafin zamansa shugaban majalisa, Lawan ya jagoranci kwamitoci masu muhimmanci kamar ilimi, aikin gona, tsaro da binciken kudaden gwamnati a majalisa.
Rahotanni sun bayyana cewa Lawan ya sayi fom din tsayawa takara domin kare kujerarsa karkashin jam’iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.
An tattaro cewa Sanata Lawan ya gabatar da kudurori sama da 200 tun lokacin da ya shiga Majalisar Tarayya a shekarar 1999, cewar Leadership.
Daga cikin kudurorin akwai gyaran dokar AMCON, dokar kiyaye bayanai, dokar jami’an zirga-zirga da kuma kudurin jami’ar fasaha ta Ogoja.

Kara karanta wannan
Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau ya janye daga neman takarar dan majalisar wakilai
Rahoton ya nuna cewa Sanata Ahmed Lawan na daga cikin ‘yan majalisar da suka fi yin magana kan muhimman batutuwan kasa duk da matsayinsa.
Ra'ayoyin wasu mutanen Yobe kan jagorancinsa
Ra’ayoyin al’ummar Yobe ta Arewa sun bambanta kan ci gaba da zaman Lawan a Majalisar Tarayya tsawon shekaru masu yawa yanzu.
Abdullahi Mohammed Nasir daga Machina ya ce Lawan ya fi mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’ummar Yobe.
Ya kara da cewa mutane da dama suna girmama Lawan saboda kokarinsa wajen tallafawa matasa da samar da damar rayuwa a yankin.
Sai dai wani mazaunin Nguru mai suna Suleiman Ubaliyo ya ce Lawan bai kawo ci gaban da ake tsammani daga gare shi ba.
Ubaliyo ya ce har yanzu yankuna da dama a Yobe ta Arewa suna fama da rashin ingantattun hanyoyi da karancin ayyukan gwamnati.

Source: UGC
Martanin masoyan Ahmed Lawan kan jagorancinsa
Sai dai magoya bayan Lawan sun ce masu suka ba su la’akari da ayyuka da tallafin da ya samar wa al’ummar mazabarsa.
Ahmad Gash Umar daga Karasuwa ya bayyana Lawan a matsayin dan siyasa mai kusanci da talakawa kuma mai taimakon matasa ta hanyoyi daban-daban.
A cewarsa, Sanatan ba ya yawan raba kudi a bainar jama’a, amma yana taimaka wa mutane ta hanyar aiki da shirye-shiryen tallafi.
Wani masoyinsa mai suna Adamu Bukar ya ce Lawan ya taimaka wajen dawo da tsarin kasafin kudin Janairu zuwa Disamba a Najeriya.
2027: Ahmed Lawan ya magantu kan zaben Tinubu
An ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya yi tsokaci kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kuri'u masu tarin yawa a yankin Arewacin Najeriya.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi hasashen tagomashin da Tinubu zai samu idan aka zo kada kuri'a a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

