2027: An Fara Ruguza Hotunan Tinubu a Kano, 'Yan Sanda Sun Yi Gargadi
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar da gargadi ga matasa kan lalata kayayyakin gwamnati da kadarorin jama’a
- Gargadin na zuwa ne bayan wani bidiyo da ta yadu a kafafen sada zumunta inda wasu matasa suka lalata allunan Bola Tinubu na 2027
- ‘Yan sanda sun ce za su hukunta duk wanda aka kama yana aikata irin wannan laifi, tare da tabbatar da cewa an fara bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta yi kira ga matasa da su kauce wa aikata barna da lalata kadarorin gwamnati ko na jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta yi gargadi tana mai cewa duk wanda aka kama da irin wannan laifi zai fuskanci fushin doka.

Asali: Facebook
Leadership ta wallafa cewa gargadin ya fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Hussaini Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fitar da sanarwar ne a ranar Asabar bayan bayyanar wani bidiyo da ya nuna matasa suna lalata allunan tallar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan zaben 2027.
A cikin sanarwar, rundunar ta bayyana aikin a matsayin rashin ladabi da ya saba doka, wanda ke haifar da barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.
Bidiyon ruguza hotunan Bola Tinubu a Kano
A cikin bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta, an ga wasu matasa suna yaga hoton allon tallan shugaban kasa Tinubu wanda ke dauke da sakon neman takara a 2027.
ASP Hussaini Abdullahi ya ce:
“Ba za a amince da irin wannan laifi ba, domin ya sabawa doka kuma yana tayar da hankalin jama’a.”
Ya kara da cewa rundunar ta riga ta fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan barna, domin tabbatar da cewa doka ta yi aikinta yadda ya kamata a kansu.
‘Yan sanda za su tabbatar da bin doka da oda
A cewar ASP Hussaini, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda.
Baya bin doka da oda, an bukaci matasan su nisanci duk wani abu da zai jawo rikici ko karya doka a cikin al’umma.
CP Bakori ya tabbatar da cewa rundunar za ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Daily Post ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Rundunar ‘yan sanda tana kira ga dukkan jama’a, musamman matasa, da su guji duk wani aiki da zai jawo lalacewar dukiyoyin jama’a ko tayar da hankali.
"Mun dauki wannan al’amari da matukar muhimmanci kuma doka za ta yi aiki a kan kowa da kowa,”

Asali: Facebook
2027: Magana kan takarar Tinubu da Shettima
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi magana kan takarar Kashim Shettima da Bola Tinubu.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce cikin shekara mai zuwa Bola Tinubu zai sanar da mataimakin shi.
Bayo Onanuga ya kara da cewa babu tabbas a kan rade radin da jama'a ke yi na cewa akwai sabani tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng