NDLEA Ta Gano Kogo da Ramin Karkashin Kasa da ake Safarar Kwaya a Kano

NDLEA Ta Gano Kogo da Ramin Karkashin Kasa da ake Safarar Kwaya a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Jami’an hukumar NDLEA sun gano tare da rusa ramuka da kogo da ake amfani da su wajen fataucin miyagun ƙwayoyi da ajiyarsu a Kano
  • NDELA ta bayyana cewa hakan na cikin kokarin ta na farautar masu safara da sayar da miyagun kwayoyi a Kano da Najeriya baki daya
  • A cewar hukumar, an gano kogon da ramukan ne a yankin Rimin Kebe na jihar, sannan an kama mutane 19 da ake zargi yayin samamen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ce ta gano wani kogo da ramukan ƙarƙashin ƙasa da ake boye kwaya.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta sanar da cewa masu sayar da kwaya na amfani da wajen a matsayin maboyar miyagun ƙwayoyi a yankin Rimin Kebe na jihar.

Kara karanta wannan

Sauki ya samu: Gwannatin Tinubu ta kaddamar da motocin CNG da na lantarki a Kano

Jami'an NDLEA sun kai samame a Kano
Jami'an hukumar NDLEA yayin farautar dilolin kwaya a kogo a Kano. Hoto: Femi Babafemi
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kan al'umma na NDLEA, Femi Babafemi, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

An gano kogon kwaya a Kano

Punch ta wallafa cewa kakakin hukumar na Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari ya ce an gudanar da samamen ne ƙarƙashin “Operation Sharar Mafaka,” wani sabon farmaki kan masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.

Muhammad-Maigatari ya ambato Kwamandan NDLEA a Kano, Dahiru Yahaya-Lawal, yana cewa gano wuraren ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da kuma ci gaba da sa ido.

A cewarsa, jami’an sun kai samame yankin Rimin Kebe ranar 4 ga Mayun 2026, inda suka tabbatar da kasancewar kogo da dama da aka gina tare da daidaita su domin zama da harkokin ciniki da ake zargin dillalan miyagun ƙwayoyi ke yi.

Ya ce wasu an sanya kayan amfanin yau da kullum a wasu daga cikin kogunan, ciki har da tabarma, matasai, faranti da kayan cin abinci, abin da ke nuna cewa ana zama a wuraren kai-tsaye.

Kara karanta wannan

An cafke dan bindiga da ya je zai karbi miliyoyin kudin fansa

Cikin kogon da NDLEA ta shiga a Kano
Kogon da ake sayar da kwaya a Kano. Hoto: Femi Babafemi
Source: Facebook

Bayanin kwamandan NDLEA

Kwamandan ya ƙara da cewa an tarwatsa da dama daga cikin kogunan da ramukan, yayin da ake shirin rusa su tare da killace sauran wuraren.

Bayan tabbatar da kama mutum 19, ya kara da cewac samamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin rundunar na ƙara kaimi wajen kawar da amfani da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa:

“Za mu ci gaba da bin waɗannan miyagun mutane duk inda suka ɓuya.

An cinnawa mata wuta a Kano

A wani labarin, mun kawo muku cewa ana zargin wata mata mai suna Maryam Muhammad ta cinnnawa kishiyarta wuta a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa matar da aka cinnawa wuta, Firdausi tana kwance a wani asibiti tana karbar magani a lokacin hada wannan rahoton.

Yayin da ya yi kokarin ceto matar da aka sanya wa man fetur, mijin matan ma ya samu rauni, inda aka bayyana cewa yanzu haka yana karbar magani a asibiti a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng