Lakurawa Sun Fara Kafa Sharudan Noma, Sun Hana Aiki da Injuna a Kebbi

Lakurawa Sun Fara Kafa Sharudan Noma, Sun Hana Aiki da Injuna a Kebbi

  • Al’ummar wasu kauyuka a Jihar Kebbi sun nemi taimakon gwamnati da sojoji kan barazanar da ’yan ta’adda ke musu a damunar bana
  • ’Yan ta’addan Lakurawa sun hana manoma amfani da injunan noma, sun ce duk wanda ya sauya daga amfani da dabbobi zai fuskanci kisa
  • Hakan na barazana ga rayuwar manoma da ci gaban noma a yankin, inda masu noma ke cikin damuwa da fargaba daga 'yan ta'addan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Al’ummar wasu kauyuka da ke gundumar Augie a Kebbi sun nuna damuwa kan yadda Lakurawa ke tarwatsa rayuwar jama’a da hana su noma cikin kwanciyar hankali.

'Yan ta’addan sun fitar da wata barazana mai tayar da hankali, inda suka gargadi manoma da cewa duk wanda ya daina amfani da dabbobi wajen noma ya koma injuna, za su kashe shi.

Lakurawa sun hana noman zamani a Kebbi
Lakurawa sun hana noman zamani a Kebbi. Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

Legit Hausa ta gano halin da ake ciki a kauyukan ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar ta haifar da firgici da rudani a tsakanin manoman yankin, musamman ma waɗanda suka rasa dabbobinsu sakamakon satar shanu da ’yan ta’addan suka dade suna yi.

Lakurawa sun kafa sharadin noma a Kebbi

Wani mazaunin garin da ya bayyana halin da ake ciki ya ce, yanzu ’yan ta’addan suna tsoma baki a harkokin noma, suna hana mutane yin amfani da sababbin hanyoyin zamani.

Mutumin ya ce:

“Yanzu haka, su ne ke sa mana dokar yadda za mu noma. Sun hana mu amfani da injuna, sun ce sai dai da dabbobi. Amma idan ka yi da dabbobi, za su zo su kwace shanun.”

Wannan hali na nuna irin yadda rayuwar al’umma ke kara shiga cikin mawuyacin hali, inda ake fargabar cewa hakan na iya hana noma gaba ɗaya a yankunan da ke fama da wannan matsala.

Manoman Kebbi sun nemi taimakon gwamnati

Bayan fuskantar wannan barazana, al’umma sun roƙi gwamnatin tarayya da jami’an tsaro da su kawo dauki cikin gaggawa don kare rayukansu da ba su damar yin noma cikin sauki.

Wasu daga cikin manoman sun ce tuni sun yanke shawarar daina noma saboda tsoron fuskantar kisa daga ’yan ta’addan Lakurawa.

Ana ganin hakan zai kara jefa yankin cikin matsalar yunwa da koma baya a harkar tattalin arziki.

Manoma sun nemi agajin gwamnati kan Lakurawa
Manoman Kebbi sun nemi agajin gwamnati kan Lakurawa. Hoto: Nasir Idris
Asali: Facebook

Sun bayyana cewa su manyan manoma ne da ke noma domin ci gaban kansu da kuma kasuwanci, amma yanzu haka babu wata dama da ta rage musu.

Majiyar ta ce jami’an tsaro sun fara duba hanyoyin da za a dauka domin dakile barazanar a jihar Kebbi.

Lakurawa sun hana sayar da shanu a Kebbi

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan ta'addan Lakurawa sun kafa dokar hana sayar da shanu a Kebbi.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan ta'adda ke cigaba da kai hare hare kan al'umma a yankunan Najeriya, musamman Arewa ta Yamma.

A jihar Kebbi, 'yan ta'addan Lakurawa sun yi barazanar kashe duk wanda ya sayar da shanunsa domin wata bukata da zai yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng