Sanata Ya Raba Miliyoyin Kudi ga Ƴan APC saboda Bikin Babbar Salla a Borno
- Wani sanata a jihar Borno ta Tsakiya ya raba wa shugabannin APC na mazabarsa miliyoyi domin tallafa musu bikin babbar sallah
- Mai taimaka masa, Usman Alkali, ya ce wannan ne karo na uku da sanatocin ya bayar da irin wannan tallafi tun bayan shiga majalisa
- Alkali ya bayyana cewa an yi rabon kudin ne domin nuna godiya ga shugabannin APC bisa kokarinsu wajen karfafa dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Sanatan mai wakiltar Borno ta Tsakiya, Kaka Shehu Lawan, ya rabawa shugabannin APC a mazabarsa makudan kudi.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa sanatan ya raba kudi har N135,650,000 domin shirin bikin babbar salla mai zuwa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa, Usman Alkali, ya wallafa a Facebook ranar Juma’a 15 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau ya janye daga neman takarar dan majalisar wakilai
Sanata ya raba makudan kudi ga shugabannin APC
Alkali ya ce wannan shi ne karo na uku da Sanata Kaka Shehu Lawan ke yin irin tallafin ga al'ummar mazabarsa wanda suke nuna jin dadi game da hakan.
Sanarwar da aka rubuta da Hausa ta bayyana cewa sanatan ya rabawa shugabannin APC a Borno ta Tsakiya kudaden ne domin taimaka musu gudanar bikin babbar salla.
Alkali ya ce an gudanar da rabon kudin ne ranar Alhamis 14 ga watan Mayu, 2026 ga shugabannin jam’iyyar APC a daukacin mazabar sanatocin domin tallafa musu kafin bikin sallah.
Ya ce:
“Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya, Sanata Kaka Shehu Lawan (SAN), ya rabawa shugabannin APC kudi har N135,650,000 domin bikin babbar salla.”
Ya kara da cewa wannan ne karo na uku da sanatocin ke yin irin wannan tallafi tun bayan zamansa dan majalisar dattawa ta kasa mai wakiltar yankin.
A cewarsa, an yi wannan tallafi ne domin nuna godiya ga shugabannin APC saboda jajircewarsu wajen kare dimokuradiyya da tabbatar da bin ka’idojinta yadda ya kamata.

Source: Original
Zaben gwamna: Dalilin janye takarar Sanata Kaka
A wani bangare kuma, Kaka Shehu Lawan ya janye daga takarar gwamnan Borno tare da marawa abokin takararsa, Mustapha Gubio, baya.
Rahotanni sun ce Gubio na samun goyon bayan gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, domin zama dan takarar gwamna a zaben da ke tafe.
Alkali ya bayyana cewa bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a Abuja, an cimma matsayar Lawan ya hakura da takarar gwamna tare da ci gaba da kujerarsa ta sanatoci.
Sanata Yari ya ba makwabtansa raguna 500
A baya, an ji cewa Sanata Abdul’aziz Yari ya rabawa makwabtansa, marasa gata, da yan gudun hijira raguna 500 domin su yi bikin babban salla ta shekarar 2023 a karamar hukumar Talata-Mafara.
Wannan kari ne a kan raguna 1,000 da shanu 400 da tsohon gwamnan na zamfara ya rabawa jiga-jigan APC a jihar yayin da ake cikin wani hali.
Mutane da dama sun nuna murna game da wannan abin alheri da ya yi masu inda suka yi ta sanya masa albarka a rayuwarsa.
Asali: Legit.ng
