Malaman Addini Sun Ayyana Ranar Azumi da Addu'oi domin Zaman Lafiya a Najeriya

Malaman Addini Sun Ayyana Ranar Azumi da Addu'oi domin Zaman Lafiya a Najeriya

  • Malaman coci Katolika na lardin Onitsha sun ware ranar Juma’a, 20 ga Yuni, 2025, a matsayin rana ta musamman don yin azumi da addu’a
  • Sun bayyana kisan da aka yi a Yelwata, Jihar Benue da Eha-Amufu, Enugu, a matsayin dabbanci da cin mutuncin ɗan Adam
  • Rahoto ya nuna cewa sun bukaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dawo da zaman lafiya a fadin ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - A wani mataki na nuna damuwa da halin rashin tsaro da ya addabi Najeriya, malaman cocin Katolika na Onitsha sun kira da a yi addu'a.

Sun kirayi mabiya addini da dukkan masu kishin Najeriya da su tashi tsaye wajen addu’a da azumi domin roƙon Allah ya kawo ƙarshen kashe-kashen da suka zama ruwan dare.

Cocin Katolika ya bukaci a yi addu'a da azumi saboda zaman lafiya
Cocin Katolika ya bukaci a yi addu'a da azumi saboda zaman lafiya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Vanguard ta ce wasu manyan jagororin cocin da ke jagorantar jihohin Anambra, Enugu da Ebonyi ne suka rattaba hannu kan wata wasiƙa da suka fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magana kan kisan Benue da Enugu

Wasiƙar da Fasto Valerian Okeke da Peter Chukwu suka sa wa hannu ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi kwanan nan a Yelwata, Jihar Benue da Eha-Amufu a Jihar Enugu.

A cewar wasiƙar,

“Muna Allah-wadai da kisan gilla da aka yi a Benue a ranar Juma’a, 13 ga Yuni, 2025.”

Sun ƙara da cewa sun damu matuka da rahotannin da suka nuna cewa irin wadannan hare-hare sun auku a Eha-Amufu, a ranar Lahadi, 15 ga Yuni.

Sun bayyana wannan zubar da jinin fararen hula a matsayin abin takaici da ban tsoro kuma yana mai kara haddasa fargaba a zukatan al’umma.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da kisan da aka yi a jihar Benue, wanda ya tashi daga Abuja zuwa jihar a ranar Laraba da ta wuce.

Sun bukaci gwamnati da ta kare rayuka

Malaman cocin sun kuma roƙi gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen kashe-kashen tare da tabbatar da adalci da zaman lafiya.

Sun jaddada cewa ba da kariya da tsaron rayukan ‘yan ƙasa ne babban nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati.

An bukaci gwamnatin tarayya ta kawo matsalar tsaro
An bukaci gwamnatin tarayya ta kawo matsalar tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Sun umarci dukkan mabiya Katolika a lardin da su sadaukar da ranar 20 ga Yuni don azumi da addu’ar neman zaman lafiya da warkar da ƙasa daga bala’in da ta ke ciki.

Punch ta wallafa cewa sun jaddada cewa dawowa ga Allah ta hanyar addu’a, adalci da haɗin kai ne kadai zai iya dawo da zaman lafiya a Najeriya.

Lakurawa sun hana noma a Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa matsalar tsaro na kara ta'azzara a yankunan Najeriya musamman a Arewa ta Yamma.

'Yan ta'addan Lakurawa sun saka dokoki da suka shafi manona a wasu yankunan jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.

Manoma a jihar sun bayyana cewa Lakurawa sun hana su amfani da kayan zamani tare da tilasta musu amfani da shanu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng