Matasan Plateau Sun Tare Motar Fasinja daga Kaduna, Sun Yi Musu Kisan Gilla
- Ana zargin wasu matasa sun kai hari kan wata mota daga Zaria a Mangu da ke jihar Plateau a Arewa ta Tsakiya
- An ce harin ya yi sanadin kashe fasinjoji bakwai da jikkata wasu da dama da ake zargin an yi saboda rashin tsaro a jihar
- An kai harin ne da misalin karfe 9:47 na dare yayin da fasinjojin ke kan hanyarsu ta zuwa bikin aure a garin Qua’an-Pan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Wani abin takaici ya faru a jihar Plateau bayan matasa sun farmaki matafiya da suka fito daga jihar Kaduna.
An ce aƙalla fasinjoji bakwai ne suka rasa rayukansu da kuma wasu da dama suka jikkata sanadin harin da aka kai.

Asali: Original
Rahoton Zagazola Makama ya ce ana zargin matasan kauyen Mangu suka kai kan wata mota dauke da yan jihar Kaduna a Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ke jawo farmaki kan fasinjoji a Plateau?
Farmakin matafiya a jihar Plateau ya zama ruwan dare tun tuni wanda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da asarar dukiyoyi.
Hakan bai rasa nasaba da nufin daukar fansa kan wadanda ba su ji na ba su gani ba duk lokacin da wani abu ya faru a jihar.
A yanzu haka, yan bindiga suna cigaba da kai farmaki kan yankunan karkara a jihar wanda ya yi sanadin rayuka da dama.
Yadda matasan Plateau suka farmaki motar fasinja
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 9:47 na dare.
Motar mai dauke da fasinjoji 28 na kan hanyarta daga Zaria zuwa Qua’an-Pan, inda akasarinsu Musulmai ne da za su halarci bikin aure.
Lokacin da motar ke wucewa a titunan Plateau, matasa suka tare ta a wajen kauyen suka kai mata mummunan hari.
Fasinjoji bakwai aka kashe nan take, daya na cikin mawuyacin hali, sannan wasu shida suka ji rauni daban-daban.

Asali: Twitter
An ceto fasinjojin da abin da ya shafa
Har ila yau, bayan farmakin da aka kai, matasan sun kuma bankawa motar wuta a wurin da lamarin ya faru.
Duk da haka, wasu shugabannin yankin sun taka rawa wajen ceton fasinjoji 14 da ba su ji ciwo ba domin dakile lamarin.
An kai wadanda suka samu raunuka asibitin gwamnati na Mangu domin ba su taimako, inda wasu suka tsaya cikin firgici da alhini wanda aka yada faifan bidiyon.
Majiyoyin ‘yan sanda a Plateau sun ce an tura jami’an tsaro zuwa Mangu kuma ana kokarin cafke wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Yan bindiga sun farmaki matafiya a Zamfara
A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan matafiya waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Zamfara.
Miyagun ƴan bindigan sun kashe direban motar bayan sun buɗe musu wuta a kan hanyar Bagaga zuwa Anka.
Bayan kashe direban motar, ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta zuwa cikin daji wanda ba a san inda suka nufa da su ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng