Ana Batun Sulhu a Katsina, Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro da Tulin Manoma
- Yayin da rahotanni ke nuna gwamnati na ƙoƙarin sulhu da ƴan bindiga, wasu sun kai hari tare da kashe jami'an tsaro huɗu
- Ƴan bindigar sun kuma kashe manoma masu ɗumbin yawa da ba a tantance ba a harin da suka kai kauyen Marmara a Malumfashi
- Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan hari babban koma baya ne ga tsarin sulhu, wanda ya kamata a sake nazari kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Ƴan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari a ƙauyen Marmara da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.
Maharan sun kashe dakarun tsaro huɗu na rundunar Community Watch Corps (CWC) da kuma tulin manoma da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu.

Asali: Original
Wani mai magana kan harkokin tsaro, Bakatsine, shi ne ya wallafa abin da ya faru a shafinsa na manhajar X ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro
Harin wanda ya auku da yammacin Litinin, ya faru ne a wajen gari, inda wasu manoma ke aiki a gonakinsu kafin 'yan bindigar su kawo farmakin ba zato ba tsammani.
Bakatsine ya rubuta a shafinsa cewa:
“Da Yammacin jiya, ƴan bindiga sun farmaki manoma a wajen garin Marmara, karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.
"An kashe jami’an CWC guda hudu da suka yi ƙoƙarin daƙile harin, an kuma kashe wasu manoma da dama, yayin da wasu kuma suka jikkata.”
Ana ƙoƙarin sulhu da ƴan bindiga a Katsina
Rahoton Leadership ya nuna cewa Gwamnatin Katsina ta fara ƙoƙarin sasantawa da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a wasu sassan jihar domin dawo da zaman lafiya.
A cewar rahoton, wasu daga cikin ƴan bindiga a Jibia, Batsari, da DanMusa sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya kuma sun mika makamansu.
Sai dai wannan sabon hari a Marmara ya haifar da fargaba da shakku a zukatan mazauna yankin, game da inganci da dorewar irin wannan yarjejeniya da ‘yan bindigar.
Wani mazaunin yankin ya bayyana damuwarsa da cewa:
“Mun fara ganin alamar zaman lafiya, amma wannan hari ya komar da mu baya. Idan har za a ci gaba da kisan bayin Allah duk da shirin sulhu, to akwai buƙatar a sake duba tsarin.”

Asali: Facebook
Wane mataki hukumomi suka ɗauka kan harin?
Har kawo yanzu rundunar ƴan sanda ko gwamnatin jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin ba, amma jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike a yankin.
Ana sa ran gwamnati da hukumomin tsaro za su dauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman yayin da damina ta karato kuma manoma ke komawa gona.
Wani ɗan yankin Ƙanƙara da ya ne a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa hare-haren ƴan bindiga na neman dawowa a Katsina.
A cewarsa, an samu sauƙi a ƴan shekarun nan duk da ba za a ce zaman lafiya ya dawo ba, amma ta'addanci ya ragu daga zuwa wannan gwamatin zuwa yanzu.
"Gaskiya wannan gwamnatin tana ƙoƙari amma idan ka duba a ƴan kwanakin ann abin na neman dawowa har ya fi da, ya kamata hukumomi su ƙara zage dantse," in ji shi.
Hatsabiban ƴan bindiga sun miƙa wuya
A wani labarin, kun ji cewa wasu manyan ƴan bindiga sun miƙa wuya tare da ajiye makamansu a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da hakan, ta ce kasurguman ƴan bindigar waɗanda suka daɗe suna aikata miyagun laifuka sun miƙa wuya ne da kansu.
An rahoto cewa bayan mika makamansu ga hukumomin tsaro, jagororin dabar ƴan bindigar sun saki duka mutanen da suka yi garkuwa da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng