Sun Sha Wuta: Jami'an Tsaro Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Katsina

Sun Sha Wuta: Jami'an Tsaro Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Katsina

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa jami'an tsaro sun samu nasara kan wasu miyagun ƴan bindiga
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan ne bayan sun kai hari a ƙaramar hukumar Safana ta jihar
  • Bayan an sha ƙazamin artabu, jami'an tsaron sun hallaka wasu daga cikin ƴan bindigan tare da ƙwato makamai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da samun nasarar hallaka ƴan bindiga 12 a wani samame da aka kai musu.

An hallaka ƴan bindigan ne a wani samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro da aka gudanar a ƙananan hukumomin Kurfi da Safana na jihar.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Katsina
Jami'an tsaro sun samu nasara kan 'yan bindiga a Katsina Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Katsina, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jami'an tsaro suka kashe ƴan bindiga

A cewar sanarwar, bayan samun sahihan bayanan sirri da sassafe, jami’an tsaro sun gaggauta tashi domin daƙile ayyukan ƴan bindiga da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.

"Ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Rahamawa da ke ƙarƙashin gundumar Kuraye a ƙaramar hukumar Charanchi da misalin ƙarfe 5:40 na asuba, inda suka jikkata wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Alhaji Danmalam, sannan suka sace shanun jama’a guda 22."
“Haɗakar jami’an ƴan sanda, sojoji, CWC da ƴan sa-kai sun bi sawun ƴan bindigan tare da yin musayar wuta da su mai tsanani a Dutsen Falale da ke tsakanin Kurfi da Safana."
“A wannan gagarumin aiki, an samu nasarar kashe ƴan bindiga 12, sannan an ƙwato bindigu AK-47 guda biyar, alburusai, da dukkan shanun da aka sace guda 22."
"Duk da murnar wannan nasara a kan ƴan ta’adda, muna jimamin mutuwar wani jarumin ɗan sa-kai ɗaya da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare al’ummarsa."

- Dr. Nasir Mu'azu

Sanarwar ta ƙara da cewa wani soja ya samu raunika a yayin artabun, kuma yana samun kulawar likitoci, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Gwamnatin jihar Katsina ta yi ta'aziyya

Haka kuma, gwamnatin jihar ta bayyana alhini kan mutuwar Alhaji Danmalam, wanda aka kai asibitin kula da lafiya na matakin farko a Charanchi, amma daga baya ya rasu sakamakon munin raunin da ya samu.

Jami'an tsaro sun samu nasara kan 'yan bindiga a Katsina
Gwamna Radda ya yi ta'aziyya kan harin 'yan bindiga Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook
“Mun yi rashin Alhaji Danmalam wanda ya rasa ransa a sakamakon harin da ƴan bindigan suka kai masa. A madadin Gwamna Dikko Umaru Radda da al’ummar jihar Katsina, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa tare da roƙon Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus."

- Dr. Nasir Mu'azu

A ci gaba da kashe miyagu

Mashakur Nasir mazaunin ruwan godiya a Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa babu wani abu da ya kamaci ƴan bindiga face a tura shi barzahu.

"Mutanen nan ba su da imani, babu tausayi ko kaɗan a zuciyarsu abin da ya kamata shi ne a tura su lahira kawai."
"Nasarar da jami'an tsaron suka samu abin a yaba ce kuma muna yi musu fatan su ci gada samu a nan gaba."

- Mashakur Nasir

Gwamnatin Katsina ta gargaɗi tubabbun ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta aika da saƙon gargaɗi ga ƴan bindigan da suka ajiye makamansu.

Gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta lamunci karya alƙawari ba daga wajen tubabbun ƴan bindigan waɗanda suka ce sun daina ta'addanci.

Ta yi gargaɗin cewa da zarar sun saɓa alƙawarin da suka ɗauka, za a koma ci gaba da yi musu luguden wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng