Nasarun MinalLah: Sojoji Sun Kashe Hatsabiban Ƴan Bindiga 16 da Suka Addabi Arewa
- Hedikwatar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun kashe shahararrun jagororin 'yan bindiga shida da mayaƙa goma a jihar Zamfara
- DHQ ta bayyana sunayen manyan 'yan bindigar da aka kashe da suka hada da Auta, Abdul Jamilu, Salisu, Babayé, da kuma ɗan Ado Alieru
- Wannan farmakin, a cewar hedikwatar tsaron ya nuna jajircewar sojoji wajen ragargazar 'yan ta'adda tare da dawo da zaman lafiya a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Alhamis, hedikwatar tsaro (DHQ) ta da cewa sojojoji sun kashe shahararrun jagororin 'yan bindiga shida da wasu mayaƙa 10 a Zamfara.
DHQ ta ce dakarun Mobile Strike Team (MST) da aka tura a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma (OPFY) ne suka kai farmakin a wurare daban-daban na jihar.

Asali: Twitter
Zamfara: Sojoji sun hallaka jagorin 'yan bindiga
Hedikwatar tsaron ta bayyana sunayen hatsabiban 'yan ta'addan da aka kashe da: Auta, Abdul Jamilu, Salisu, Babayé, da wani daya da ba a gano ko waye ba, a cewar rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa, daraktan yaɗa labarai na hedikwatar, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa an kashe Sale Ado Madele (Sarki), babban ɗan jagoran 'yan bindiga, Ado Alieru.
A cewar sanarwar Manjo Janar Markus:
"Dakarun Mobile Strike Team (MST) a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma (OPFY) sun kashe gungun 'yan ta'adda yayin wani gagarumin farmaki a kusa da garin Kunchin Kalgo a karamar hukumar tsafe ta jihar Zamfara a ranar 10 ga Yuni 2025."
"Daga cikin waɗanda aka kashe akwai wani shahararren ɗan ta'adda da aka sani da Auta, tare da abokan aikinsa Abdul Jamilu da Salisu."
Sojoji sun dukufa wajen kashe 'yan ta'adda
Sanarwar ta ce waɗannan 'yan ta'addan suna da alaƙa da ayyukan tashin hankali da ta'addanci da dama a cikin yankin.
Hedikwatar tsaron ta kuma jaddada cewa wannan farmakin ya nuna himmatuwar sojoji na gurgunta masu aikata laifuffuka, tare da dawo da zaman lafiya da tsaro a Zamfara.
"Bayanan sirri na farko sun nuna an kashe ƙarin jagororin 'yan ta'adda biyu, ciki har da wani da aka tabbatar da sunansa Babayé, a yayin farmakin."
- Manjo Janar Markus Kangye.

Asali: Twitter
Dakarun MST da OPFY sun hallaka miyagu 10
A sanarwar DHQ da Legit Hausa ta gani a shafin hedikwatar na X, Manjo Janar Markus Kangye ya kara da cewa:
"A wani ci gaban, sojoji sun kashe Sale Ado Madele (wanda aka fi sani da Sarki), babban ɗan jagoran 'yan bindiga da aka sani Ado Alieru.
"Har Ila yau, dakarun MST da OPFY sun kuma kashe ƙarin 'yan ta'adda goma waɗanda suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga."
Janar Markus Kangye ya ce an yi imanin cewa 'yan ta'addan wani ɓangare ne na ƙungiyar da Dogo Sule ya haɗa don kai hare-hare a yankunan Zamfara.
Karanta sanarwar a kasa:
Dan ta'adda Umar Black ya mika wuya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu manyan kwamandojin 'yan bindiga sun miƙa wuya a Katsina, biyo bayan wani sasanci da aka yi tsakaninsu da mutanen gari.
Daga cikin jiga-jigan da suka miƙa wuya akwai Abu Radda, Maikada da Tukur 'Dan Najeriya, waɗanda kowannensu ke da ɗaruruwan mabiyansa.
Sun nemi gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina da a daina kashe su ba tare da laifi ba, da kuma samar musu da ruwan sha, makarantu da sauran abubuwan more rayuwa.
Asali: Legit.ng