Gwamnatin Sakkwato Ta Bude Kofar Sulhu ga 'Yan Ta'adda, Ta Gindaya Sharudan Karban Tuba

Gwamnatin Sakkwato Ta Bude Kofar Sulhu ga 'Yan Ta'adda, Ta Gindaya Sharudan Karban Tuba

  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana da cikakken kudiri na kawo karshen rashin tsaro ta hanyar tattaunawa da ‘yan bindiga
  • Gwamnatin ta gindaya sharadi cewa sai ‘yan bindiga sun ajiye makami tare da amincewa da zaman lafiya kafin a fara tattaunawa da su
  • Mashawarcin Gwamna a kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ya ce an sha kawo karshen kashe-kashe ta hanyar sulhu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Gwamnatin Jihar Sakkwato ta jaddada aniyarta na samar da zaman lafiya mai dorewa da kuma tabbatar da tsaro a jihar duba da halin fargaba da jama'a ke ciki.

Mashawarcin Gwamna a kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya ne ya bayyana hakan, yana mai cewa gwamnati a shirye take ta bi tattauna da 'yan bindiga da suka addabe su.

Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu
Gwamnatin Sakkwato ta amince da fara tattaunawa da 'yan bindiga Hoto: @ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Jaridar Punch News ta wallafa cewa Kanal Usman mai ritaya ya ce gwamnati a bude kofar da za ta bayar da damar tattaunawa da ‘yan bindiga, wadanda suka tuba da gaske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Sakkwato ta fadi sharadin sulhu

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin Sakkwato ta bayyana cewa dole ne sai ‘yan bindigar da ke son sulhu sun nuna cikakken niyyar ajiye makamansu.

Sannan sai sun amince da tabbatar da cewa za su zauna lafiya da sauran al’umma kafin a shiga tattaunawa da su.

Kanal Ahmed Usman mai ritaya ya ce:

“Muna maraba da duk wani mataki da zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankinmu.
Ya kamata mu gane cewa, a tarihi, an shawo kan da dama daga cikin rikice-rikice ta hanyar tattaunawa ba nuna karfi ba."
A nan Sakkwato, a shirye mu tattauna da duk wani dan bindiga da ya nuna cikakken niyya ta tuba da rungumar zaman lafiya.”

Sakkwato: Kanal Usman ya yabi shugaba Tinubu

Kanal Usman mai ritaya ya yaba wa Shugaban kasa Bola Tinubu, hafsoshin tsaro da duka jami’an tsaro a fannoni daban-daban bisa yadda suke kokarin tabbatar da doka da oda a jihar da ma kasa baki daya.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Gwamnatin Sakkwato ta yabi shugaban kasa kan wanzar da tsaro a jihar Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ya ce:

“Ina yaba wa Kwamandan dakarun soji na kasa, hafsoshin tsaro, kwamandojin tsaro da duka jami’an da ke bakin aiki bisa kokari da sadaukarwar da suke yi.

Mai ba wa Gwamnan shawara ya kuma yi addu’ar rahama ga rayukan dakarun da suka rasa rayukansu a fafatawa da ‘yan ta’adda.

Ya kara da addu'ar Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ba iyalai da yan uwan dakarun da suka rasu hakuri, inda ya ce babban rashi ne wanda ba zai misaltu ba.

Gwamnatin Katsina da zauna da 'yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa Ado Aliero, shahararren ɗan bindiga da ya addabi Arewa maso Yamma, ya ce zai yi wahala a bar shi ya ci gaba da ta’addanci muddin ana kiransu yan ta'adda.

Ado Aliero ya bayyana cewa yawancin matasan da suka shiga ta’addanci sun shiga ne saboda rashin adalci da halin da ake ciki wanda ya jefa su cikin kunci duk da rashin jin dadin iyayensu.

A zaman sulhu da aka yi a Katsina, Aliero ya dage cewa sulhu na gaskiya da dawowar zaman lafiya zai samu ne kawai idan aka daina nuna musu wariya da kiran su da sunan ‘yan ta’adda

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.