Hausawa na Zanga Zanga bayan Dan Sanda Ya Kashe dan Arewa a Oyo

Hausawa na Zanga Zanga bayan Dan Sanda Ya Kashe dan Arewa a Oyo

  • Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan Arewa sun barke da zanga-zanga a jihar Oyo bayan wani jami'in dan sanda ya kashe dan acaba
  • A lokacin hada wannan rahoton, bincike ya nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi domin nuna fushi kan kashe dan uwansu
  • Legit ta tuntubi kakakin 'yan sandan jihar Oyo, Olushola Olayinka, inda ya yi karin bayani game da halin da ake ciki a halin yanzu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Wasu 'yan Arewacin Najeriya, musamman masu sana'ar acaba sun barke da zanga-zanga a jihar Oyo bayan kashe wani dan uwansu.

Wasu rahotanni sun nuna cewa wanda aka kashe din ya dauko hanya ne daga Kudancin Najeriya zuwa jihar Zamfara da ke Arewacin kasar.

Zanga zangar Hausawa a Oyo
Hausawa na zanga-zanga bayan kashe dan acaba a Oyo. Hoto: Legit
Source: Original

Biyo bayan faruwar lamarin, Legit Hausa ta tuntubi kakakin 'yan sandan jihar, Olushola Olayinka domin sanin matakan da jami'an tsaro suka dauka.

Kara karanta wannan

An cafke mai taimakon 'yan bindiga a Katsina, an same shi da kayan tsafi

An kashe dan Arewa a Oyo

An ruwaito cewa wasu jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya a Jihar Oyo sun kashe wani mai tuka babur mai suna Yahuza Umar.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar, 2 ga Afrilun 2026, a yankin NIKO da ke kan babbar hanyar Iseyin-Oyo a Jihar Oyo.

Yadda aka kashe dan Arewa a Oyo

A cewar wani shaidar gani da ido, Yahuza da ya fito daga Jihar Zamfara yana kan hanyarsa ta komawa Arewa ne lokacin da wani jami’in da ke bakin hanya ya buge shi da bayan bindiga, lamarin da ya janyo mutuwarsa.

Legit ta tabbatar da cewa an ajiye gawarsa a asibitin FADOK da ke Iseyin, yayin da lamarin ya haifar da tashin hankali tsakanin Hausawa da mazauna yankin a Jihar Oyo.

Hausawa sun yi zanga-zanga

A lokacin hada wannan rahoto, al’ummar Hausawa a Iseyin, musamman masu tuka babura, sun tare babbar hanya da baburansu domin nuna fushinsu.

Kara karanta wannan

2027: Alamu sun nuna Kwankwaso da Obi za su fita daga jam'iyyar ADC

Yadda Hausawa suka toshe hanya a Oyo
Wata hanya da Hausawa suka toshe yayin zanga-zanga a Oyo. Hoto: Legit
Source: Original

Karin rahotanni sun tabbatar da cewa sun tare kofar ofishin ‘yan sanda, abin da ya hana zirga-zirgar mutane da abubuwan hawa a yankin da abin ya faru.

Bayanin rundunar 'yan sanda

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Oyo, Olushola Olayinka, ya ce an shawo kan lamarin a halin yanzu.

Ana fatan cewa jami'an tsaro za su fitar da cikakken bayani game da abin da ya faru da kuma sanar da jama'a matakan da za ta dauka kan jami'in da aka ce ya yi kisan.

An kama mai taimakon 'yan ta'adda

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta tabbatar da kama wani matashi mai shekara 28 bisa zargin taimakon 'yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa matashin da aka kama mai suna Abdullahi Abdullahi ya amasa cewa yana ba 'yan bindiga bayanai domin garkuwa da mutane.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi kira ga mutanen Katsina da su rika ba jami'an tsaro bayanai game da duk wanda ake zargi yana aikata laifuffuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng