'Zai Wahala Mu Bari': Ado Aliero Ya Faɗi Abin da Zai Sa Su Cigaba da Ta'addanci

'Zai Wahala Mu Bari': Ado Aliero Ya Faɗi Abin da Zai Sa Su Cigaba da Ta'addanci

  • Dan bindiga, Ado Aliero ya yi jawabi a taron sulhu da aka gudanar a yau Asabar a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya domin samar da zaman lafiya
  • Aliero ya ce ba za su daina tashin hankali ba muddin ana kiran su da ‘yan ta’adda yayin da yake magana a taron zaman lafiya
  • Ya bayyana cewa rashin adalci da halin kuncin rayuwa ne ya tilasta wa matasa daukar makami duk da iyayensu ba su amince ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Shahararren dan bindiga, Ado Aliero yana daga cikin wadanda suka halarci taron sulhu a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.

Aliero ya bayyana cewa muddin ana kiran su da ‘yan ta’adda, ka da a sa ran su daina tashin hankali wanda ya jawo rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

Jawabin Ado Aliero yayin taron sulhu
Ado Aliero ya bukaci mutunta juna tsakaninsu da al'umma. Hoto: @ZagazOlamakama.
Asali: Twitter

Katsina: Dalilin taron sulhu da aka yi

Aleiro ya fadi hakan ne a lokacin wani zaman tattaunawar sulhu da aka gudanar a karamar hukumar Danmusa, cewar rahoton Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da taron ne a jihar Katsina, inda ya wakilci kungiyarsu tare da yin jawabi na musamman da kiran a samar da zaman lafiya.

A cewarsa, yawancin matasan da suka shiga ta’addanci sun shiga ne saboda rashin adalci da halin da ake ciki wanda ya jefa su cikin kunci.

An yi zaman sulhu a jihar Katsina
Ado Aliero ya yi jawabi a taron sulhu a Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Abin da ke damun iyayensu yan bindiga

Ado Aliero ya kara da cewa, iyayensu ba su goyon bayan abubuwan da suke yi ba, amma halin rayuwa ne ya tilasta musu daukar makami da aikata laifi.

Ya ce:

“Iyayenmu ba sa jin dadin abin da muke yi, mu ma ba lalle bane muna so. Mun fi son zaman mutunci da doka ta tsaya tsayin daka.
“Muddin har yanzu ana kiranmu da ‘yan ta’adda, to kada ku sa ran za mu daina halayen ‘yan ta’adda."

Aliero ya fadi sharaɗin watsar da ta'addanci

Aliero ya dage cewa sulhu na gaskiya da dawowar zaman lafiya zai samu ne kawai idan aka daina nuna musu wariya da kiran su da sunan yan ta’adda.

Taron da aka gudanar a Danmusa na daga cikin kokarin sulhu da ake yi tsakanin jami’an tsaro, shugabannin al’umma da kungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankin.

Shugabannin gargajiya, masu ruwa da tsaki na al’umma da jami’an gwamnati na kara kokari domin kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin Arewa maso Yamma.

An cafke iyalan Ado Aliero a Saudiyya

A baya, kun ji cewa ana zargin hukumomin Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargi da kasancewa uwa da matar jagoran ‘yan bindiga, Ado Aliero kan zarginsa.da kai hare haren a Arewa.

Majiyoyi sun ce an kama su ne a birnin Madina bayan wani samame da aka yi bisa bayanan leƙen asiri daga hukumomin tsaro.

Ado Aliero na ɗaya daga cikin manyan 'yan bindiga da Najeriya ke nema ruwa a jallo saboda hare-hare da garkuwa da bayin Allah wanda ya daidaita al'ummomi da jawo asarar rayuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.