Kiristoci Sun Fusata da Bayahude Ya Ci Zarafin Kirista a Isra'ila a Bidiyo
- Wata mata mai hidimar addinin Kirista ta jikkata bayan wani Bayahude ya ci zarafin ta a birnin Jerusalem
- Mutumin ya ka mata hari kusa da Mount Zion a Jerusalem, lamarin da ya tayar da kura sosai a fadin duniya gaba ɗaya
- ‘Yan sanda sun kama mutumin mai shekara 36 bayan ana zarginsa da tura matar ƙasa tare da dukan ta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jerusalem, Israel - Wani Bayahude mai shekara 36 ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zarginsa da kai hari kan wata mata.
Majiyoyi suka ce mutumin ya ci zarafin matar mai hidimar addinin Kirista kusa da Mount Zion a Jerusalem.

Source: Getty Images
Wani bidiyo da The Guardian ta wallafa a YouTube ya nuna yadda ake cin zarafin matar lamarin ya tada hankula sosai musamman daga al'ummar Kiristoci da shugabanninsu.
An ci zarafin mai hidimar coci a Isra'ila
Rahotonni sun bayyana cewa matar, wacce ke aiki da makarantar koyar da addinin Kiristanci a Faransa.
An tabbatar da cewa matar tana tafiya ita kaɗai lokacin da aka farmake ta daga baya wanda lamarin ya tayar da hankali.
‘Yan sanda sun ce mutumin ya tura matar ƙasa sannan ya rika dukanta da ƙafa kafin wani mutum ya shiga tsakani ya ceci ta daga harin.hk
Rahotanni sun tabbatar da cewa matar ta samu raunuka a fuska, amma ba a samu barazanar rasa ranta ba bayan an kai ta asibiti domin kulawa.
Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, yayin da ake ci gaba da yi masa tambayoyi kan musabbabin harin da ake zargi.
Masu bincike suna duba yiwuwar cewa tsattsauran ra’ayin addini ne ya haddasa harin, musamman ganin wurin da abin ya faru da kuma irin tufafin wanda ake zargin.

Source: Getty Images
Alwashin da yan sanda suka dauka
‘Yan sandan kasar Isra’ila sun yi tir da harin tare da jaddada cewa ba za su lamunci cin zarafin shugabannin addini ko masu ibada ba a ƙasar, cewar rahoton BBC News.
Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta bayyana harin a matsayin abin kunya, tana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin addini da lafiyar al’ummomi.
Fasto Olivier Poquillon ya ce harin yana nuna yadda ake ƙara nuna ƙiyayya ga malaman addinin Kirista a yankin cikin ‘yan kwanakin nan da suka gabata.
Lamarin ya sake fito da rikice-rikicen addini da siyasa da ke yawan faruwa a Jerusalem, inda ake nuna damuwa kan zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai.
Kiristoci: Faransa ta ja kunnen Isra'ila
Mun ba ku labari a baya cewa kasar Faransa ta yi Allah-wadai da karuwar hare-haren da ake yi wa Kiristoci da aka ce gwamnatin Isra'ila karkashin Netanyahu ne ke kai wa.
Rahotanni sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot ne ya yi magana bayan wani mummunan hari da aka kai.
Hakan na zuwa ne yayin da Isra'ila ke kai hare-hare Lebanon, inda kungiyar Hezbollah ke mayar da martani duk da cewa an tsagaita wuta.
Asali: Legit.ng

