Gwamnatin Kano Ta Yi Martani ga Zargin Karbo Bashin $6.6m a cikin Shekaru 2

Gwamnatin Kano Ta Yi Martani ga Zargin Karbo Bashin $6.6m a cikin Shekaru 2

  • Gwamnatin Kano ta yi watsi da zargin karbo bashin sama da $6m daga waje, tana cewa siyasa ce kawai wasu suka shirya da gangan
  • Darakta Janar na Hukumar Kula da Basussuka, Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce ba a karbo wani sabon bashi ba tun bayan hawansu mulki
  • Gwamnati ta bukaci kungiyar APC dake zargi da ta bayyana takardun shaida idan da gaske suke Abba Kabir Yusuf ya karbi kudin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin jihar Kano ta musanta zargin da cewa ta sake karbo sabon bashi da ya kai $6.6m, tana mai cewa wannan zargi ba gaskiya.

Wannan ya biyo bayan zarge-zargen da kungiyar APC Patriotic Volunteers, wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Alhaji Usman Alhaji, ke jagoranta, ya yi.

Gwamnatin Kano ta musanta karbo bashi
Gwamnatin Kano ta ce ba ta karbo sabon bashi ba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Darakta Janar na Hukumar Kula da Basussuka ta Kano, Dr. Hamisu Sadi Ali, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa babu wani sabon bashi da aka karbo daga watan Yuni zuwa Disamba 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano ta caccaki tsohon SSG

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Dr. Hamisu ya soki tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano bisa nuna cewa bai san dokar hukumar kula da bashi ba.

Ya ce kowa na da masaniyar gwamnatinsu ta jam'iyyar APC ce ta kafa dokar hukumar a shekara ta 2021.

Ya ce:

“Idan har yana cewa bai san da dokar ba, ya kamata mu tunatar da shi da sashi na 4(b) na dokar, wanda ke bai wa hukumar damar karbar bashi a madadin gwamnati, amma karkashin ka’idoji da takardu na musamman.”

Gwamnatin Kano ta kalubalanci jam'iyyar APC

Darakta Janar ya kalubalanci rukunin APC da su fito da hujjoji masu inganci da ke tabbatar da zargin da suke yi.

Ya ce:

“Ya kamata su bayyana sunan wanda ya bayar da bashin, yarjejeniyar raba bashin, manufar bashi, tsarin biyan sa, da ko bashi ne daga kungiyoyi da dama ko kasashen waje.”
“Yanzu mutane sun waye, sun san bambanci tsakanin gaskiya da shirin yaudara da siyasa ke haifarwa.”
Gwamnati ta kalubalanci APC
Gwamnati ta nemi APC ta gabatar da hujjar basussukan da ta karbo Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya kara jaddada cewa gwamnatin Kano a karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ba ta karbo wani bashi daga ƙasashen waje da kungiyar APC ke yadawa ba.

Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce:

“Wannan zargi ba shi da tushe kwata-kwata, kuma an shirya shi ne domin yaudarar al’umma."

An zargi gwamnatin Kano da karbo bashi

A baya, kun ji cewa Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta yi zargin cewa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta karɓi bashin $6.6m daga ƙasashen waje.

Shugaban ƙungiyar, Usman Alhaji, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Kano ranar Laraba, inda ya bukaci sanin inda aka kai kudin.

Ya bayyana cewa duk da karɓar wannan bashi, gwamnati ta kuma ciwo wasu basussuka, amma har yanzu babu wani aiki da ya bayyana ko aka gabatar na kashe kudin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.