Dimokuraɗiyya: Atiku Ya Fadi Fargabarsa, Yana Ganin za a Fara Mulkin Kama Karya a Najeriya
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana fargabar halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Najeriya
- Ya bayyana cewa dimokuraɗiyya na cikin haɗari, ana murƙushe ‘yan adawa, ana ba wa abokan shugaban ƙasa manyan kwangiloli
- Atiku ya kara da cewa wannan matsala ce ta sa samar da hadakar jam'iyyun adawa domin ta kwato Najeriya daga fadawa wahala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda mulkin dimokuraɗiyya ke tabarbarewa a Najeriya.
Atiku Abubakar ya kara da cewa ƙasar na dab da fadawa cikin mulkin kama-karya, inda ake ƙoƙarin kawar da jam’iyyun adawa daga fagen siyasa.

Asali: Facebook
Tsohon mataimakin shugaban ya bayyana haka ne a sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook domin tunawa da ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku: "Ana dab da fara mulkin kama-karya"
Arise News ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda ake kokarin ruguza dimokuraɗiyyar da aka sha wahala ana tattalawa.
Ya ce:
“Yau Najeriya na dab da rugujewa, ana kokarin maye gurbin dimokuraɗiyya da mulkin kama-karya."
"Wadanda suka sadaukar da rayukansu a June 12 ba don mu koma cikin azabar zalunci da tsadar rayuwa suka yi hakan ba."
Atiku ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki da gwamnatin tarayya na amfani da karfi da iko wajen murkushe muryar ‘yan adawa.
Ya ce ana baiwa ‘yan uwa da abokan arzikin shugaban ƙasa manyan kwangiloli, ba tare da bin ka’ida ba.
"Gwamnati ta taɓarɓara dimokuraɗiyya," Atiku
Atiku ya zargi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauya akalar mulkin ƙasa zuwa abin da ya kira “ƙasƙantar da dimokuraɗiyya.”
Ya ce a maimakon ƙarfafa ɗan ƙasa, gwamnati tana amfani da manufofi wajen jefa tsoro a zuciyoyin jama'a, musamman yan adawa.

Asali: Facebook
Ya ce:
“’Yan Najeriya na fama da wahalar rayuwa, an bar su ga wahala yayin da wasu ƙalilan ke morewa. Wannan ya sabawa duk wani abu da ranar dimokuraɗiyya ke wakilta."
Ya kuma goyi bayan yunkurin gina ƙawancen jam’iyyun adawa, yana mai cewa hakan ba son mulki ba ne, amma “kokari ne na kare martabar dimokuraɗiyya.
Atiku ya ƙara da cewa ya zama wajibi a dawo da mulkin ƙasa hannun ‘yan ƙasa, domin kare makomar ƙarni mai zuwa.
"Tinubu na kawo romon dimokuraɗiyya," Dankabo
A wani labarin, mun wallafa cewa fitaccen dan siyasa, Ahmed Dankabo ya bayyana cewa Arewa na cin gajiyar sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa.
Dankabo, wanda daya ne daga cikin cikin ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2023 ya bayyana cewa ana jin dadin salon mulkin APC.
Dankabo ya jaddada goyon bayansa ga Shugaba Tinubu, yana mai cewa ya yarda da ƙwarewarsa tun kafin ya hau kujerar mulki, kuma kowa ya shaida nasarar da ake samu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng