Jigon ADC Ya Tona Bakar Maganar da Obi Ya Fada game da Atiku a Sirrance
- Jigon ADC a Najeriya ya bayyana abin da ɗan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya fada masa kan Atiku Abubakar
- Dan siyasar ya ce Obi ya fada masa cewa ya taba kin amincewa da shawararsa ta hada kai da Atiku saboda ya fi shi a siyasance
- Ya ce ya ba Obi misalan siyasar Ghana da Amurka, amma tsohon gwamnan ya nace cewa yana da karbuwa fiye da Atiku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jigo a jam'iyyar ADC, Dele Momodu, ya yi magana game da zaben shugaban kasa na 2027 a Najeriya.
Dele Momodu ya bayyana cewa Peter Obi ya taba kin amincewa da shawararsa ta hada kai da Atiku Abubakar a siyasa.

Source: Facebook
Abin da Obi ya fada kan Atiku Abubakar
Momodu ya ce Obi ya shaida masa cewa ya fi Atiku farin jini a tsakanin al'umma, cewar rahoton Punch.
Ya bayyana cewa idan aka tambayi Obi, zai tabbatar bai yi masa karya ba ko kadan a kalamansa.
Momodu ya ce:
“Peter shi ne ɗan siyasa kaɗai da ya taɓa ziyartar gidana a London, Ghana da Lagos, a ɗaya daga cikin ziyarar, na gaya wa Peter cewa, ‘Ka yi ƙoƙarin yin aiki tare da Atiku.’

Source: Twitter
Shawarar da Momodu ya ba Obi
Momodu ya ce Peter Obi ne kadai dan siyasar da ya taba ziyartar gidajensa da ke London, Ghana da Lagos.
Ya ce a daya daga cikin ziyarar, ya shawarci Obi da ya yi kokarin hada kai da Atiku domin amfanin siyasar nan gaba.
Momodu ya ce ya kawo misalin John Mahama na Ghana, wanda watakila bai zama shugaban kasa ba da bai fara zama mataimakin Atta Mills ba.
Ya kuma kawo misalin Amurka, inda Joe Biden ya dawo ya zama shugaban kasa bayan ya nuna kwarewa duk da tsufansa.

Kara karanta wannan
Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Tinubu, Kwankwaso, Atiku, Obi kudin goro kan zaben 2027
“Na kuma ba shi misalin Amurka, inda duk da cewa Biden ya fi Obama shekaru sosai, amma daga baya ya dawo ya zama Shugaban Ƙasa saboda ya nuna ƙwarewa da cancantarsa.
“Kai dai ka taɓa zama gwamnan jiha ne kawai, amma Peter ya gaya mini cewa ya fi Atiku farin jini. Na rantse da Allah. Idan ka gan shi, ka tambaye shi ko na yi masa ƙarya.”
A cewarsa, Obi ya taba zama gwamnan jiha ne kawai, amma ya dage yana ikirarin cewa ya fi Atiku karbuwa a idon jama'a, cewar Daily Post.
Momodu ya kuma yi tsokaci kan yanayin siyasar kasar, yana cewa akwai masu ruwa da tsaki da dama da ke fargabar karuwar tasirin Tinubu.
Atiku ya magantu da aka ceto dalibai
Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi murna da ceto mutum 360 da aka sace a Ngoshe da ke jihar Borno.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yabawa sojoji da jami’an tsaro kan nasarar da suka samu na ceto mutanen bayan watanni fiye da biyu.
Ya ce hakan ya nuna cewa dakarun tsaron Najeriya za su iya magance duk wata barazana matukar aka samar masu da kayan aiki.
Asali: Legit.ng
