Uba Sani da Wasu Fitattun Ƴan Najeriya 71 da Tinubu Ya Karrama a Ranar 12 ga Yuni
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama wasu fitattun 'yan Najeriya, wadanda suka rasu, da wadanda ke da rai, bisa gudunmawarsu ga ci gaban Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tinubu ya karrama wadannan 'yan mazan jiyan, ciki har da Janar Shehu Musa Yar'Adua, a yayin da yake jawabin ranar dimokuradiyya ga 'yan majalisar tarayya a Abuja a ranar Alhamis.

Asali: Twitter
Tinubu ya jinjinawa hangen nesan Buhari
Mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar sababbin kafofin sada zumunta, Olusegun Dada, ya wallafa cikakken jawabin shugaban kasar na ranar dimokuradiyya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mun ruwaito cewa, Tinubu wanda ya fara yabawa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shaidawa 'yan majalisar dattawan da na wakilai cewa:
"Tun daga shekarar 2018, muke gudanar da bikin ranar dimokuraɗiyya a irin wannan rana; domin tunawa da sadaukarwar maza da matan da suka yi gwagwarmaya don dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.
"Bari in yaba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa hangen nesansa na gyara wani kuskure da aka yi a baya, ta hanyar mayar da 12 ga Yuni zuwa ranar dimokuraɗiyya.
"Haka kuma, ya amince a hukumance cewa marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola da mataimakinsa, Babagana Kingibe, ne suka ci zaɓen 12 ga Yunin 1993."
Tinubu ya yabawa saudarwar 'yan mazan jiya
A jawabin, Tinubu ya ci gaba da cewa:
"Duk da cewa Cif MKO Abiola shi ne babban jigo na ranar 12 ga Yuni, kada mu manta da dogon jerin waɗanda su ma suka cancanci a kira su jarumai na dimokuraɗiyyar Najeriya.
"Dole ne mu yaba wa jarumtar Hajiya Kudirat Abiola da Pa Alfred Rewane, waɗanda jami'an zaluncin soja suka kashe su.
"Haka nan muna tunawa da ɗimbin masu fafutukar kare haƙƙin bil'adama, ƴan jarida, da ƴan siyasa da aka ɗaure, aka kora, aka jefar, aka azabtar kuma aka daka musu duka ta hanyar mulkin soja.
"Muna tunawa da Cif Anthony Enahoro, Kwamanda Dan Suleiman, Cif Abraham Adesanya, Ayo Adebanjo, Cif Gani Fawehinmi, Balarabe Musa, Ganiyu Dawodu, ɗan jarida Bagauda Kaltho, da Kwamanda Ndubuisi Kanu.
"Na ambaci waɗannan sunaye ba don nuna wariya ko rage gudummawar kowane ɗan adam ba, amma don buga misali, ta hanyar waɗannan ƴan jarumai."

Asali: Twitter
Tinubu ya karrama fitattun 'yan Najeriya
A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar, an ga wani dogon jerin sunayen fitattun 'yan siyasa da Tinubu ya karrama da lambobin yabo daban daban.
Ga cikakken jerin fitattun 'yan Najeriya da Tinubu ya karrama, da lambar yabon da aka ba su:
Lambar girmamawa ta GCON
- Rt. Hon. Abbas Tajudeen
- Senator Godswill Obot Akpabio
- Wole Soyinka
- Shehu Musa Yar'Adua
Lambar girmamawa ta CON
- Alao Aka Bashorun
- Alhaja Sawaba Gambo
- Barrister Felix Morka
- Bayo Onanuga
- Bishop Matthew Hassan Kukah
- Chief Frank Kokori
- Dr. Amos Akingba
- Dr. Beko Ransome-Kuti
- Dr. Edwin Madunagu
- Dr. Kayode Shonooki
- Dr. Nurudeen Olowopopo
- Femi Falana, SAN
- Fredrick Fasehun
- Governor Uba Sani
- Ken Saro-Wiwa
- Ledum Mitee
- Mobolaji Akinyemi
- Olawale Osun
- Prof. Bayo Williams
- Prof. Humphrey Nwosu
- Prof. Julius Ihonvbere
- Prof. Olatunji Dare
- Prof. Segun Gbadegesin
- Prof. Shafideen Amuwo
- Professor Festus Iyayi
- Rear Admiral Ndubuisi Kanu
- Sen. Ayo Fas anmi
- Sen. Polycarp Nwite
- Senator Shehu Sani
- Tokunbo Afikuyomi
- Tunji Alausa
Lambar girmamawa ta CFR
- Alhaji Balarabe Musa
- Chief Bola Ige
- Kudirat Abiola
- Pa Alfred Rewane
- Pa. Reuben Fasoranti
- Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu
- Sen. Abu Ibrahim
- Sen. Ame Ebute
- Senator Jibrin Ibrahim Barau
Lambar girmamawa ta OON
- Abdul Oroh
- Ayo Obe
- Bagauda Kaltho
- Bamidele Aturu
- Baribor Bera
- Barinem Kiobel
- Chima Ubani
- Daniel Gbooko
- Dapo Olorunyomi
- Emma Ezeazu
- Felix Nuate
- John Kpuine
- Kunle Ajibade
- Labaran Maku
- Luke Aghahanenu
- Nick Dazang
- Nordu Eawo
- Nosa Igiebor
- Paul Levera
- Sam Amuka Pemu
- Saturday Dobee
- Seye Kehinde
Batutuwan da Tinubu ya tabo a ranar dimokuradiyya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki a ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ya bayyana irin rawar da majalisar ta taka wajen kare dimokuraɗiyya, musamman a lokutan ƙalubale kamar yunƙurin neman wa'adin mulki na uku a shekarar 2006.
Daga karshe, Tinubu ya kuma yi alƙawarin cewa ba zai taɓa goyon bayan kafa gwamnatin jam’iyya guda ba a Najeriya, duk da rade-radin da ake yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng