'Dan Ta'adda Umar Black da Wasu Jagororin 'Yan Bindiga Sun Mika Wuya a Katsina

'Dan Ta'adda Umar Black da Wasu Jagororin 'Yan Bindiga Sun Mika Wuya a Katsina

  • Wasu manyan kwamandojin barayin daji sun mika wuya a jihar Katsina bayan sulhu da wata kungiya ta shiga tsakaninsu da al’umma
  • Daga cikin jiga-jigan da suka mika wuya akwai Abu Radda, Maikada da Tukur 'Dan Najeriya, kowannensu na da daruruwan mabiyansa
  • Sun nemi gwamnati ta daina kashe su ba tare da laifi ba tare da samar musu da ruwan sha, makarantu da sauran abubuwan more rayuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Wata kungiya da ke aiki a yankunan karkarar jihar Katsina ta bayyana cewa wasu daga cikin shahararrun jagororin ‘yan bindiga a jihar sun mika wuya.

Shugaban kungiyar, Kwamared Hamisu Sai’idu Batsari, ya ce sulhun da suka yi da ‘yan bindigar ya kawo sauyi, inda wasu daga cikinsu ke rike da makamansu don kariya daga abokan gaba.

Radda
'Yan bindiga sun mika wuya a jihar Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

A wata tattaunawa da ya yi da BBC, Sai’idu Batsari ya bayyana cewa ‘yan bindigan ne da kansu suka nemi sulhu, sabanin yadda aka saba a baya ana nemansu da alkawurra kafin su amince.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun mika wuya a jihar Katsina

Daga cikin kwamandojin da suka mika wuya akwai Abu Radda, Maikada, Umar Black da Tukur Dan Najeriya, wadanda kowannensu ke da daruruwan matasa karkashinsu.

Kwamared Hamisu Sai’idu Batsari ya bayyana cewa:

“Kowannensu musamman Abu Radda na da yaran da suka kai 500 karkashinsa. Su Tukur Mairakumi da Maikada da Dan Najeriya suna da daruruwan mabiyansu,”

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadannan kwamandojin na rike da makamai ne domin kare kansu daga sauran barayin daji da ba su yarda da sulhu ba.

Yadda 'yan bindiga suke nemi sulhu

Kwamared Hamisu ya ce sulhun da suka cimma a yanzu ya bambanta da wanda aka saba, domin a wannan karon ‘yan bindigan ne da kansu suka nemi zaman sulhu.

Ya ce hakan na nuna alamar nasara a kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin da ta’addanci ya dabaibaye shekaru da dama.

Daga cikin sharuddan da aka amince da su akwai dakatar da ta’addanci da kuma sakin dukkan mutanen da suka kama – ba sai na yankin Katsina kadai ba.

Bukatar tubabbun 'yan bindiga wajen gwamnati

A bangaren ‘yan bindigan, sun bukaci gwamnatin da ta samar musu da ruwan sha, makarantu da sauran abubuwan more rayuwa domin sauya rayuwarsu.

Haka zalika sun bukaci a daina kama su da kashe su ba tare da wata hujja ba. Idan aka kama su da laifi, a kai su kotu a yi musu shari’a bisa doka.

Yan bindiga
Yan bindiga sun bukaci a musu adalci bayan sun tuba. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar ya ce:

“Ana buƙatar a tabbatar da adalci tsakaninsu da sauran al’umma,”

'Yan bindiga sun sace matar basarake

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan wani basarake a jihar Kaduna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun sace matar basaraken tare da wata 'yar shi a lokacin da suka kutsa gidan na shi.

Legit ta rahoto cewa mutanen garin sun yi kokarin ceto matan cikin dajin da aka gudu da su, sai dai basu samu nasara ba kuma 'yan bindigar sun harbe daya daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng