Ranar Dimokuraɗiyyar: An Roƙi Tinubu Ya Maido Fubara Kujerar Gwamnan Ribas
- Jigon PDP ya bukaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yafewa Siminalayi Fubara kamar yadda ya yafewa Babajide Sanwo-Olu a Legas
- Cif Bode George ya ce maido da Fubara zai nuna girmamawa ga waɗanda suka yi sadaukarwa don assasa dimokuraɗiyya a Najeriya
- A ranar 18 ga Maris ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da gwamna, Fubara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jigon jam’iyyar PDP, Bode George, ya roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya maido da Siminalayi Fubara, kujerarsa ta gwamnan jihar Ribas.
Ya ce kamata ya yi shugaban kasar ya maido Fubara da aka dakatar, a matsayin wani bangare na bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni 2025.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa a cikin wata wasika da jigon ya aikawa Tinubu, ya ce tun da shugaban ya yafewa Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ya dace a nuna irin wannan ga Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bode George ya roki Tinubu ya yafewa Fubara
The Punch ta ruwaito tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa daga yankin kudu maso yamma, Bode George, ya ce ya kamata Tinubu ya mutunta ranar dimokuraɗiyya.
Ya ce:
“A ranar 12 ga Yuni, za mu yi bikin ranar Dimokuraɗiyya. Wannan rana ce da ke tuna mana ma’anar dimokuraɗiyya na gaske.
“Tun da Tinubu ya yafewa Sanwo-Olu, to yana da muhimmanci, a yafe wa Fubara kuma a bar shi ya koma ofis. Ina magana ne a matsayina na dattijo.”
Bode George: "Tinubu ya hidimtawa dimokuraɗiyya"
Bode George ya ce ya kamata shugaban ƙasa Tinubu ya girmama waɗanda suka rasa rayukansu a gwagwarmayar kafuwar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Asali: Instagram
Ya kara da cewa:
“Tinubu ya shiga ƙungiyar NADECO don yaƙi da mulkin kama-karya. Wasu daga cikin waɗanda suka yi gwagwarmaya tare da shi sun rasu. Ba laifinsa ba ne cewa shi ya tsira.
“Don haka ya kamata ya gode wa Allah, ya girmama tarihin waɗanda suka mutu saboda dimokuraɗiyya, sannan ya maido da Fubara ofis nan take. “Ina kuma roƙonsa, da ya tuna sadaukarwar Herbert Macaulay, baturen da ya kafa jam’iyyar siyasa ta farko a Najeriya a 1922, ya maido da Fubara ofis.”
A ranar 18 ga Maris, Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas mai arzikin mai, saboda rikicin siyasa da rashin daidaito a jihar. Haka kuma, ya dakatar da gwamna Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da 'yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida a matakin farko.
Tinubu ya karya al'adar ranar dimokuraɗiyya
A baya, mun ruwaito cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karya al’adar gabatar da jawabi ta kai tsaye ga ‘yan ƙasa a ranar 12 ga Yuni, Ranar Dimokuraɗiyya.
A yau Alhamis, 12 ga Yuni, Najeriya na bikin cika shekaru 26 tana turbar mulkin dimokuraɗiyya ba tare da an samu kutsen mulkin soja ko katsewar tsarin ba.
Duk shekara, shugabannin ƙasa kan gabatar da jawabi ga al’umma da 7.00 na safe, a kowace ranar dimokuraɗiyya, amma wannan karon, an soke hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng