Dangote zai Girgiza Harkar Man Fetur da Manyan Sauye Sauye a Najeriya

Dangote zai Girgiza Harkar Man Fetur da Manyan Sauye Sauye a Najeriya

  • Aliko Dangote ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su sanar da wani babban sauyi a bangaren kasuwancin mai a Najeriya
  • Ya ce ba rage farashi ba ne nufinsu a wannan karon, sai dai sauya fasalin harkar kasuwancin man fetur a ƙasa baki daya
  • Dangote ya bayyana cewa aikin da suka fara a matatar mai da ke Lekki zai haifar da juyin juya hali a bangaren masana’antu da tattali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Shahararren attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya ce kamfaninsa na shirye-shiryen girgiza tsarin kasuwancin mai da kawo sauye-sauye da za su kawo cigaba mai ɗorewa.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai, bayan ziyarar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai matatar mansa a Lekki, jihar Legas.

Dangote zai kawo sauyi a Najeriya
Dangote zai kawo sauyi harkar mai a Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Asali: UGC

Punch ta wallafa cewa sauyin da za su sanar nan ba da jimawa ba, ba rage farashin man fetur ba ne kai tsaye, sai dai sauya gaba ɗaya tsarin bangaren rarraba man fetur a ƙasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu sauya tsarin mai gaba ɗaya" - Dangote

Rahoton jaridar Daily Post ya nuna cewa Dangote ya yi bayani kan sauye sauyen ne bayan da Bola Tinubu ya ziyarci matatarsa da ke Legas.

Dangote ya ce:

"Yanzu da shugaban ƙasa ya ziyarce mu kuma ya ƙara mana ƙwarin guiwa, zamu sanar da ku wani sauyi nan ba da jimawa ba. Wannan sauyi da muke shirin yi zai girgiza ƙasa baki ɗaya."

Ya ƙara da cewa aikin matatar zai shiga wani mataki mai faɗi, wanda zai zarce duk wani abu da ake gani a yanzu.

Maganar Dangote kan zuba jari a Najeriya

Dangote ya tabbatar da cewa za su cigaba da zuba jari a bangarori da dama domin habaka tattalin Najeriya.

Ya bayyana cewa manufofin shugaban ƙasa Tinubu sun sauƙaƙa wa masana’antu da kuma janyo masu zuba jari, wanda hakan ya taimaka wajen kawo manyan tsare-tsare.

Ya nuna godiya bisa yadda gwamnati ke fifita abubuwan da ake samarwa a cikin gida fiye da na ƙetare, musamman a harkar zuba jari da kasuwanci.

Dangote ya taimaka kan rage dogaro da ketare

Dangote ya bayyana cewa burin kamfaninsa shi ne samar da dukkan kayayyakin da Najeriya ke buƙata a cikin gida, ta yadda za a rage dogaro da ƙasashen waje.

Ya ce:

"Mun riga mun kai ga hakan a sashen siminti da takin zamani. Najeriya ta zama mai isar wa kanta da kayayyakin nan kuma tana fitar da su zuwa ƙasashen waje."
Dangote zai rage dogaro da kashen waje
Dangote zai rage dogaro da kashen waje a Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

A cewar Dangote, yanzu haka matatarsa ta fara fitar da kaya zuwa ƙasashe kamar Amurka da Saudiyya.

An kira Dangote 'shugaba' a gaban Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Aliko Dangote ya ci gyaran mai gabatar da taro yayin da Bola Tinubu ya ziyarci matatar shi.

Mai gabatar da taron ya kira Dangote da 'shugaba' a gaban shugaban kasa Bola Tinubu yayin da ya kira shi ya yi jawabi.

Sai dai cikin barkwanci Alhaji Aliko Dangote ya ce ai shugaba daya ne a wajen, yana ishara da Bola Ahmed Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng