Dangote Ya Rage Farashin Mai zuwa N825, amma 'Yan Kasuwa na Sayarwa Sama da N900

Dangote Ya Rage Farashin Mai zuwa N825, amma 'Yan Kasuwa na Sayarwa Sama da N900

  • Duk da cewa Dangote ya saukar da farashin mai zuwa tsakanin ₦875 da ₦905, gidajen mai sun ki sauya farashin da suke sayar da man
  • Matatar Dangote ta rage farashin har sau shida a 2025, amma ana ci gaba da sayar da mai tsakanin ₦890 zuwa ₦910 a gidajen mai
  • Masu gidajen mai sun koka da saukar farashi ba tare da sanarwa ba, inda suka cewa hakan yana jawo masu asaran mai da rashin riba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Duk da ci gaba da rage farashin man fetur da matatar man Dangote ke yi, har yanzu gidaje mai na ci gaba da sayar da fetur a farashi mai tsada.

A jiya Alhamis muka ruwaito cewa matatar Dangote ta sake rage farashin man fetur mai zuwa N825, wanda ke nufin cewa 'yan Najeriya za su sayi lita daya a kan N875-N905.

Gidajen mai sun ki saukar da farashin fetur duk da Dangote ya rage kudin lita sau 6
Mutane na layin sayen fetur a wani gidan mai. Hoto: Petrol Stations NG
Asali: UGC

Dangote ya rage farashin fetur zuwa N875-N905

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa matatar ta sanar da yadda farashin lita zai kasance a kowacce shiyya kamar haka:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • ₦875 a Legas
  • ₦885 a yankin Kudu maso Yamma
  • ₦895 a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya
  • ₦905 a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas

Sanarwar matatar ta bayyana cewa farashin zai shafi dukkanin abokan hulɗarta shida; MRS, AP (Ardova), Heyden, Optima Energy, Techno Oil, da Hyde Energy.

Dangote ya bukaci sauran ‘yan kasuwa da su shiga cikin wannan tsari na hadin gwiwa domin nuna goyon bayansu ga manufar gwamnati na saukaka wa 'yan Najeriya.

Lokuta 6 da Dangote ya rage farashin mai

Rahotannin da aka tattara game da wannan lamarin sun bayyana cewa duk da rage farashin da Dangote ke yi, har yanzu man fetur na da tsada a gidajen mai.

Bincike ya nuna cewa, Dangote ya rage farashin man sau da dama cikin shekarar 2025, kuma adadin raguwar ya kai N195 gaba ɗaya.

A watan Janairu, Dangote ya sanar da cewa zai sayar da litar man a N955. A Disambar 2024 kuwa, ya rage farashin daga N970 zuwa N899.50 a matsayin “garabasar karshen shekara”.

A ranar 1 ga Fabrairu, Dangote ya rage farashin da N60, inda lita ta koma N890, sannan a 26 ga Fabrairu, ya sake rage farashin da N65, lita ta zama kimanin N825.

Wannan na nufin daga farashin N950 da ake biya a Janairu, yanzu ya koma N825, wanda ke nuna raguwar N125 cikin kwanaki 26.

Sanarwa ta wancan lokaci ta ce rage farashin zai sanya 'yan Najeriya su rika sayen mai a tsakanin N860 da N865 a Legas.

Matatar man Dangote ta rage kudin litar man fetur kusan sau 6 a cikin shekarar 2025
Shugaban rukunonin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Bloomberg
Asali: Facebook

Gidajen mai sun ki rage farashin fetur

Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, gidajen mai ba su sauya farashinsu ba, inda lita ɗaya ke ci gaba da sayarwa tsakanin ₦890 zuwa ₦910 a Legas.

Duk da cewa masu sayar da man sun nuna jin daɗi kan raguwar farashin, sun bayyana damuwa dangane da yadda aka sanar da raguwar farashin ba tare da isasshen lokaci ba.

A watan Afrilu, lokacin da Dangote ya saukar da farashi sau biyu, rahotanni sun nuna cewa masu sayar da mai sun yi asarar biliyoyin Naira saboda saukar farashin da bai zo da shiri ba.

Sakataren watsa labarai na ƙungiyar masu sayar da man fetur mai zaman kansu (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya yi gargadin cewa masu sayar da mai na fuskantar hangen asara fiye da riba a wannan rikicin farashi.

Dangote da kamfanoni sun kulla alakar fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matatar Dangote da ke Legas ta kulla yarjejeniya da kamfanonin Ardova da Heyden domin samar da fetur a farashi mai sauki.

Wannan haɗin gwiwar ya bai wa kamfanin MRS Oil damar sayar da lita ɗaya na fetur a kasa da ₦930, sakamakon tsarin sayayya da yawa da aka aiwatar.

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, wannan dabarar ta taimaka wajen rage karancin mai da saukaka wa jama’a samun fetur a gidajen mai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.