Jerin Hadiman Tinubu da Suka Ajiye Mukami a Shekara 2 da Hawansa Mulki
- Tun bayan hawan Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, akalla masu ba shi shawara uku sun yi murabus daga mukamansu
- Masu murabus din sun bayar da dalilai daban-daban, daga matsin lamba na iyali zuwa rashin jituwa da tsarin siyasa da manufofin gwamnatin tarayya
- Ficewar wasu daga cikinsu, musamman Hakeem Baba-Ahmed ta janyo muhawara kan yadda gwamnati ke tafiyar da mulki da kare darajar dimokuradiyya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A cikin shekara biyu da fara mulki, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rasa akalla uku daga cikin manyan hadimansa, wadanda suka ajiye aiki bisa dalilai daban-daban.
Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jama’a da kwararru kan yadda gwamnatin ke tafiyar da harkokin siyasa da tattalin arziki.

Asali: Facebook
A wannan rahoto, Legit Hausa ta tattaro muku jerin hadiman da suka yi murabus da dalilan da suka sanya su daukan matakin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Ngelale ya ajiye aiki saboda matsalar lafiya
A ranar 7 ga Satumba, 2024, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa inda ya bayyana cewa yana bukatar kula da lafiyar iyalansa.
Daily Trust ta wallafa cewa Ajuri Ngelale ya bayyana haka ne da kansa inda ya ce:
"Na ajiye aikina daga yanzu...saboda matsalar lafiya da ta shafi iyalina."
Ya godewa Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi, kuma ya bayyana fatan komawa hidimar kasa idan abubuwan sun daidaita.
Aikinsa Ngelale ya tsaya saboda bukatun gida, ba tare da suka kai tsaye ga gwamnatin ba kuma har yanzu bai sake magana kan yiwuwar dawowa aiki ba.

Asali: Twitter
2. Matsalolin ƙasa sun sa Hakeem Baba murabus
A watan Afrilu 2025, Hakeem Baba-Ahmed ya ajiye aikinsa bayan watanni kalilan da shigar sa cikin gwamnatin Tinubu.
Punch ta wallafa cewa da farko ya ce dalilinsa na "kashin kai ne," amma daga bisani ya bayyana cewa ya gaji da rashin gamsuwa da yadda gwamnati ke fuskantar matsalolin Najeriya.
A wata hira da Channels TV, ya ce:
"Ban yi nadamar shiga gwamnatin ba, amma da a ce hannun agogo zai koma baya, ba zan sake shiga gwamnatin ba. Gwamnatin ba ta nuna kwazo wajen gyara ƙasa ba."
Ya kara da cewa talauci da rashin tsaro na ƙaruwa, yana nuna fargaba kan rashin kulawa da muhimman al’amura da suka shafi rayuwar al’umma.

Asali: Twitter
3. Aliyu Audu ya yi murabus kan dalilan siyasa
A ranar 8 ga Yuni, 2025, Aliyu Audu ya miƙa takardar murabus daga ofishinsa, yana mai cewa siyasar da gwamnati ke bi yanzu ba ta dace da manufarsa ta dimokuraɗiyya ba.
Vanguard ta wallafa cewa Aliyu Audu ya nuna damuwa da haɗin gwiwa tsakanin Tinubu da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
A cewarsa:
“Na yarda da manufofin tattalin arziki na Tinubu, amma siyasar da ake bi yanzu ta sabawa burina na gaskiya da dimokuraɗiyya.”
Ya bayyana damuwa kan yunkurin mayar da Najeriya zuwa jam’iyya ɗaya, yana mai cewa hadin gwiwar da ake yi da Wike na da illa ga tsarin siyasa mai kyau.

Asali: Facebook
Tinubu ya ce ya yi kokari a shekara 2
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ya yi kokari a shekara biyu da ya yi a kan mulkin Najeriya.
Shugaban kasar ya bayyana cewa ya yi kokari wajen daukar matakan da ska farfado da tattalin arzikin Najeriya musamman hauhawar farashi.
Rahoton Legit ya nuna cewa Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin jawabi da ya yi wa 'yan Najeriya yayin bikin babbar sallah a jihar Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng