An Fadi Sunayen Mutum 13 da Ake Zargi da Sace wa Dangote Kayan Naira Biliyan 4
- Rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wani ɗan kasar India da wasu mutane 12 a gaban kotun tarayya da ke Ikoyi, Lagos
- Ana zargin mutanen da haɗin baki da karkatar da dizal mai darajar sama da Naira biliyan 4 mallakar kamfanin Dangote
- Wadanda ake tuhuma sun musanta laifuffukan da ake zarginsu da su, yayin da kotu ta dage shari’ar zuwa watan Yuli mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rundunar ‘yan sanda na sashen yaki da damfara da ke Ikoyi, jihar Legas, ta gurfanar da wani ɗan kasar India da wasu mutane 12 bisa zargin karkatar da dizal na kamfanin Dangote.
Wadanda aka gurfanar sun hada da ma’aikatan kamfanin Dangote da kuma wakilan wasu kamfanonin sufuri.

Asali: Getty Images
Punch ta wallafa cewa sun hada da wandanda aka ɗauka aiki domin jigilar dizal daga rumbunan Dangote zuwa masana’antunsa da ke Ibese da Obajana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tuhumar su da laifuffuka 16 da suka shafi hada baki, karkatar da dizal ba bisa ka’ida ba, da kuma karɓar kudin da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Dangote: Sunayen mutanen da ake zargi
Wadanda aka gurfanar su ne Ikechukwu Obi, Chigozie Osukwu, Ukaegbu Chukwuma, Umeh Ugochukwu, Emmanuella Akamadu (mace).
Haka zalika akwai Zango Umar, Emmanuel Oku, Shaibu Michael, Lucky Otoide, Mmaduabuchi Okezuonu, Ephraim Kanakapudi, da Omojowo Emmanuel.
Daga cikin su akwai ma’aikatan Dangote, su ne: Emmanuella Akamadu, Emmanuel Oku, Zango Umar, Lucky Otoide, da Ephraim Kanakapudi.
Sauran sun kasance ma’aikata ne daga kamfanonin Arigen Integrated Ltd, Obat Ltd, Amaiden Energy Ltd, Regal Gate Ltd, Alkham Ltd, Prestige Ltd da Opetrus Global Ltd.
Ana zargin an karkatar da lita miliyan 1.53
Lauyan mai gabatar da kara, M. Y. Bello, ya bayyana wa kotu cewa laifukan sun faru ne tsakanin Janairu 2022 da Disamba 2023.
Ya ce wakilin Regal Gate, Alkham da Prestige (Mai suna Tukur Shamsudden) – kamfanonin da Dangote ya ɗauka aiki – ya karkatar da dizal lita 1,530,893 da darajarsa ta kai N1.53bn.
Haka nan, Omojowo Emmanuel da ke matsayin Manajan Opetrus Global, ya karkatar da lita 2,455,229 na dizal da darajarsu ta kai N2.45bn.
Wadanda ake zargi sun musanta laifinsu
Leadership ta wallafa cewa M. Y Bello ya bayyana cewa laifukan da aka aikata sun sabawa sassan dokar kasa.
Sai dai dukkan mutum 13 da aka gurfanar sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su, kuma lauya ya sanar da kotu cewa wasu daga cikinsu sun riga sun samu beli tun farko.
A zaman da kotu ta yi ranar Talata, an sake karanto musu sabuwar tuhuma, wadda ta haɗa da kama wani ɗan Indiya da wasu mutum biyu.

Asali: Getty Images
Alkalin kotu, Mai shari’a Deinde Dipeolu, ya dage cigaban shari’ar zuwa ranar 22 da 23 ga Yuli, 2025 domin cigaba da sauraron ƙarar.
Yadda Dangote ya ba 'yan Najeriya aikin yi
Kamfanin Dangote, wanda Aliko Dangote ke jagoranta, ya kasance daya daga cikin manyan masana'antu masu samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya fiye da dubban kamfanoni a cikin gida.
Ta hanyar masana’antunsa na siminti, sukari, gari, taliya da man fetur, Dangote ya ba dubban mutane aikin yi kai tsaye da kuma ba kai tsaye – daga ma’aikata a matakin ƙasa zuwa injiniyoyi da direbobi.
Masana’antun Dangote na taka rawa wajen inganta tattalin arzikin Najeriya ta hanyar rage dogaro da kayayyakin waje, samar da kudaden shiga da kuma bunkasa harkokin sufuri da kasuwanci a fadin kasar.
Baya ga haka, Dangote na daga cikin fitattun masu zuba jari da ke daukar nauyin ayyukan jin kai a fannoni daban-daban.
Sai dai, duk da wannan gudunmawa, ana yawan samun rahotanni na satar kayayyaki ko dukiyar kamfanin daga ma’aikata ko abokan hulda.
Wannan yana nuna irin kalubalen da masu kamfanoni ke fuskanta wajen amincewa da amintattu a harkokinsu.
A wannan lamari da aka bankado, an zargi wasu da karkatar da dizal da darajarsa ta haura Naira biliyan 4 – dukiya da za ta iya tallafa wa daruruwan ma’aikata ko ci gaban masana’antu. Wannan satar ta zama wani abin takaici ga wani kamfani da ke fafutukar gina kasa.
Dangote zai kawo sauyi a harkar mai
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya ce nan ba da jimawa ba zai kawo sauyin da zai girgiza harkar man fetur a Najeriya.
'Dan kasuwar ya bayyana haka ne bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar shi a makon da ya wuce.
Aliko Dangote ya kara jaddada muhimmancin amfani da kayayyakin da aka kera ko samar a Najeriya domin habaka tattali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng