Gwamna Dikko Radda Ya Yi Wa Katsinawa Alkawari kan Rashin Tsaro
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar jaje kan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Dutsinma
- Dikko Radda ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin kawo ƙarshen barnar ƴan bindiga
- A yayin ziyarar, Radda ya tattauna da wasu mutanen ƙauyen domin samo mafita kan hanyar da gwamnati za ta taimaka wajen samar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ba mutanen jihar tabbaci kan matsalar rashin tsaro.
Gwamna Dikko Radda ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki muhimman matakai don kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga a fadin jihar.

Asali: Facebook
Ya yi wannan alƙawari ne a ranar Juma’a yayin wata ziyarar jaje da ya kai ƙauyen Gobirawa da ke ƙaramar hukumar Dutsinma, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya je jajen harin ƴan bindiga
Gwamna Radda ya kai ziyarar ne bayan harin da ƴan bindiga suka kai a makon da ya gabata wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu bayin Allah.
A yayin ziyarar, Gwamna Radda ya umarci shugaban ƙaramar hukumar Dutsinma da ya zaɓo mutane biyar daga cikin al’ummar garin.
Ya buƙaci a zaɓo mutanen ne domin halartar muhimmin taro da za a gudanar kan yadda gwamnatin jihar za ta tallafa wa ƙoƙarin samar da tsaro na cikin gida.
"Bayan da gwamnati ta samu rahoton sirri kan shirin harin, sai ta aika da jami’an tsaro zuwa ƙauyen."
"Amma sai dai ƴan bindigan sun kai harin ne bayan da jami’an tsaron suka bar garin."
- Gwamna Dikko Radda
Dikko Radda ya faɗakar da al'umma
Yayin da yake nuna alhini game da wannan mummunan lamari, gwamnan ya buƙaci jama’ar ƙauyen da su kasance masu faɗakarwa da lura da duk wani da ake zargi da ba da bayanai ga ƴan bindiga.
Ya jaddada muhimmancin rawar da al’umma ke takawa wajen yaƙi da rashin tsaro.

Asali: Facebook
Gwamnan ya samu tarba daga ɗan majalisa mai wakiltar Dutsinma a majalisar dokokin jihar, Mohammad Khamis; Hakimin Yandakan Katsina, Alhaji Sada Sada, shugaban ƙaramar hukumar Dutsinma, Kabir Shema, da wasu manyan jami’ai daga yankin.
Radda ya je ziyarar gani da ido
A wani cigaban kuma, gwamnan ya ziyarci aikin gina makarantar sakandare ta zamani da ake kira Smart School da ke Radda a ƙaramar hukumar Charanci.
Ya umurci kamfanonin da ke aikin ginin makarantar da su tabbatar da inganci da gaggauta kammala aikin cikin lokaci.
Gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa game da jinkirin da wasu daga cikin masu kwangila ke yi wajen gudanar da aikin.
Wannan aikin makarantar Smart School da ke Radda na daga cikin guda uku da gwamnatin Radda ke ginawa a kowace mazaɓar domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yara, musamman ƴaƴan talakawa.
Sarkin Daura ya faɗi matsalar da ta fi ta tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq, ya nuna takaicinsa kan yadda ake sare itace ba bisa ƙa'ida ba.
Sarkin Daura ya bayyana cewa sare itace ba bisa ƙa'ida ba ya fi ta'addanci illa saboda barazanar da yake yi wa muhalli.
Alhaji Faruq Umar-Faruq ya bayyana cewa masarautar Daura ta ɗauki sare itace ba bisa ƙa'ida ba a matsayin babban laifi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng