Duk da Halin da Katsina Ke ciki, Sarkin Daura Ya Fadi Abin da Ya Fi Ta'addanci Illa
- Sarkin Daura a jihar Katsina, Alhaji Faruq Umar-Faruq ya bayyana abin da ya fi ta’addanci muni saboda illarsa ga muhalli
- Ya ce majalisar masarautar Daura na daukar matakai kan sare itatuwa a matsayin babban laifi da ke bukatar tsananin hukunci
- Daraktan Hukumar 'Great Green Wall' ya ce za su raba tsabar dabino miliyan 5 a jihohin Arewa 11 domin dakile kwararowar hamada
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Daura, Katsina - Sarkin Daura da ke jihar Katsina, Alhaji Faruq Umar-Faruq ya yi magana kan halin da suke ciki na matsaloli.
Sarkin ya ce sare itatuwa ba tare da ka’ida ba ya fi ta’addanci saboda barazanar da yake wa muhalli.

Asali: Facebook
Sarkin Daura ya koka kan sare itatuwa
Sarkin ya fadi haka ne a Daura a ranar Juma'a lokacin da Darakta-Janar na Hukumar 'Great Green Wall', Saleh Abubakar, ya kai masa ziyara, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sarkin, majalisar masarautar ta dauki sare itatuwa a yankin a matsayin babban laifi saboda hadarinsa ga al’umma.
Mai martaba ya ce tun da dadewa masarautar ta dauki sare itace a matsayin laifi kamar kashe dan Adam.
Saboda muhimmancin dasa itatuwa, masarautar ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama yana sare itatuwa.
Ya kara da cewa mafi yawan matsalolin muhalli a wasu yankuna na faruwa ne saboda sakaci wajen sare bishiyoyi.
Umar-Faruq ya ce masarautar Daura ce ta fara dasa bishiyoyi sosai fiye da kowanne wuri a fadin kasar nan.
Ya ce:
"Masarauta za ta hada kai da hukumar wajen rabon tsabar dabino domin rage rashin aikin yi da kuma matsalar rashin tsaro."

Asali: Twitter
Rokon da Sarkin Daura ya yi ga al'umma
Sarkin ya kuma yi alkawarin fadakar da jama’a kan muhimmancin dasa bishiyoyi don rage yawan sare itatuwa da kuma kare muhalli.
Ya bukaci hukumar ta mayar da hankali wajen yaki da sare itatuwa saboda illa ga muhalli, ciki har da yaduwar hamada da sauyin yanayi.
A baya, Darakta janar na hukumar ya ce sun kawo ziyara ne domin samun goyon bayan sarki wajen dakile yaduwar hamadar Sahara.
A cewarsa, yaduwar hamada na lalata gonaki da halaka dabbobi, saboda haka ya kamata jama’a su rungumi dasa itatuwa.
"Idan aka dakile hakan, za mu samu isasshen ruwan sama da amfanin gona zai karu, kuma tattalin arziki zai bunkasa.
"Yanzu muna fama da zafi fiye da da, kuma dasa bishiyoyi ne kadai mafita."
- Cewar Saleh Abubakar
Ya ce a hanyarsa ta zuwa Daura, ya ji dadin ganin filayen dasa bishiyoyi da ke kan hanya.
Sarkin Daura ya tube rawanin Dagaci
Kun ji cewa bayan korafe-korafe, Sarkin Daura, Alhaji Faruq Faruq ya dauki mataki kan dagacin kauyen Mantau, Iliya Mantau.
Sarkin ya ɗauki matakin ne saboda wasu zarge-zargen da ake yi masa na garkuwa da mutane da kuma fyade ga wata mata.
Dagacin shi ke sarautar kauyen Mantau a Yarmaulu ya rasa rawaninsa bayan matasa sun yi zanga-zanga kan jinkiri wajen daukar mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng